Wani ganau ya sheda wa manema labarai cewa; ‘Yan uwansa suna cikin wadanda abin ya fara da su.
Yace; bayan an kwashe musu Shanu sun bi duk ka’idar dokar hana kiwo ta Jihar Benue, sun kuma biya naira miliyon 27, bayan sun karbo shanunsu suka ce babu mota a barsu su kora shanunsu amma aka ki yarda.
- Ana Zargin Sojoji Da Kisan Fulani Makiyaya 39 A Nasarawa
- Dan Gwamnan Jihar Nasarawa Mai Shekaru 36, Hassan Sule Ya Rasu
Bayan sun kwaso shanun suka zo Akwanaja suka sauke domin tura su zuwa cikin Nasarawa kawai sai suka ji kara ta ko’ina hade da walkiya nan da-nan sai ga gawarwakin mutane da shanu zube a kasa. Cewar Isa Aliyu Musa
Da yake jawabi, Alhaji Bello Badejo, yace; ya kamata a sani fa su Fulani suna da ‘yancin yin kiwo a ko’ina cikin fadin kasar nan bama jihar Benue ka dai ba.
Yace; mu bama goyon bayan duk wani Bafillatanin da zai janyo rigima. Duk wani Bafullatanin da ya janyo rigima muna goyon bayan a hukunta shi.
Sannan ya yi kira ga Gwamnatin jihar da ta tarayya da ta gargadi gwamna Oton na Jihar Benue.
Ya kuma bukaci lallai a mayar da kudi naira miliyon 27 da aka karba a wajen wadanan Fulanin da sunan kudin Belin shanunsu.
A wannan harin an kashe mutum 37 an kuma yi wa mutane 17 raunuka, don akwai Dattajon da aka kashe masa yara 9 rigis lokaci guda.