Wani harin bam da ake zargin sojoji ne suka kai, ya yi sanadiyyar mutuwar Fulani makiyaya akalla 39, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a wani kauye da ke Jihar Nasarawa.
A cewar Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Nasarawa, Maiyaki Muhammad Baba, lamarin ya faru ne a kauyen Rukubi wanda ke daf da iyakar jihar da Jihar Benuwe, inda aka kirga gawarwakin makiyaya 27 da kuma dabbobi masu tarin yawa, ko da ya ke kungiyar Miyetti Allah ta ce adadin ya kai mutane 39.
- Majalisa Ta Tabbatar Da Arase A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Kula Da ‘Yansanda
- Kan Wane Dalili Google Ya Ce ‘Dangote Ne Mamallakin Nijeriya’ ?
Wata majiya ta rawaito Kungiyar Miyetti Allah na zargin cewa jirgin sojojin sama ne ya suka kaddamar da harin kan makiyaya, batun da har zuwa yanzu sojojin ba su musanta ba ko kuma bayar da ba’asi kan dalilin farmakin.
MACBAN cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakinta, Muhammad Nura ta bukaci sojojin su bayar da ba’asin kan kisan Makiyayan wadanda ke kan hanyarsu ta dawowa daga biyan tarar Naira miliyan 29 da Jihar Benuwe ta sanya musu bayan karya dokar kiwo.
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule wanda ya sha alwashin gudanar da binciken kan lamarin, ya ce an yi amfani da jirage marasa matuka wajen kai harin a ranar Laraba, wanda ya kashe makiyaya 38 tare da shanunsu.
Gwamnan, ya bukaci a kwantar da hankali a yankin da lamarin ya faru wato kan iyakar jihohin Nasarawa da Benuwe yankin da ake yawan samun rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a Nijeriya.