Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi jawabi a gun budadden taron muhawara kan batun samar da zaman lafiya, wanda majalisar ta gudanar a jiya Alhamis 26 ga watan nan, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi a nuna fifiko kan samar da ci gaba a yayin da ake raya ayyukan zaman lafiya.
Zhang Jun ya bayyana cewa, gina zaman lafiya wani muhimmin bangare ne na samar da dauwamammen zaman lafiya, kuma ya fi muhimmanci da yin fice a halin da ake ciki yanzu. Ya kara da cewa, ya kamata aikin samar da zaman lafiya ya karkata ga samar da ci gaba.
Ga kasashe da yawa, ci gaba shi ne babbar mafita wajen tinkarar kalubale daban-daban. Akwai bukatar a nuna fifiko kan ci gaba don samar da zaman lafiya, kuma a mai da hankali kan amfani da albarkatu wajen kawar da talauci, da kare rayuwar jama’a, da yada ilimi, da kiwon lafiyar jama’a da sauran fannoni. Kana da nuna goyon baya ga raya masana’antu, da sha’anin noma, da zamanintar da muhimman ababen more rayuwa.
Ya ce kamata ya yi kasashe masu ci gaba su cika alkawuran da suka dauka, na ba da tallafin ci gaba da samar da kudade don shawo kan kalubalen sauyin yanayi, tare kuma da biyan basussukan da suka ci a tarihi.
A nasu bangaren, ya kamata hukumomin hada-hadar kudi na kasa da kasa su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, su shiga cikin aikin samar da zaman lafiya, da gudanar da hadin kai.
Zhang Jun ya kuma kara bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ba da goyon baya ga aikin samar da zaman lafiya, ta hanyar aiwatar da hakikanin matakai, da kuma ba da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)