• English
  • Business News
Saturday, June 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyautatuwar Matakan Kandagarkin COVID-19 Sun Taimaka Wa Birnin Yiwu Wajen Farfado Da Kasuwanci

by Kande Gao
2 years ago
in Daga Kasar Sin
0
Kyautatuwar Matakan Kandagarkin COVID-19 Sun Taimaka Wa Birnin Yiwu Wajen Farfado Da Kasuwanci
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

Nailah, ’yar kasuwa ce dake da shaidar ’yar kasa ta Jamus da Italiya. A farkon watan Janairun bana, ta dawo garinta na biyu, wato birnin Yiwu na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, wanda ake kiransa da Babban Shagon Duniya.

Jim kadan da saukarta daga jirgin sama, Nailah ta nufi babbar kasuwar kasa da kasa ta Yiwu ba tare da bata lokaci ba, domin haduwa da abokan kasuwancinta da ba su hadu da juna ba har na tsawon shekaru biyu da suka gabata.

  • Mataimakin Wakilin Kasar Sin Dake MDD Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Taimakawa Mali Kara Karfin Yaki Da Ta’addanci
  • Masani: Sin Za Ta Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasa Ci Gaban Duniya A Shekarar 2023

Nailah ta fara kasuwancinta a birnin a shekarar 2017, inda hajoji iri daban daban, da aikin rarraba kayayyaki cikin sauki, da kyakkyawan muhallin kasuwanci, suka ba ta babbar damar habaka kasuwancinta.

Hakika dai, dimbin baki ’yan kasuwa sun dawo kasar Sin kamar yadda Nailah ta dawo, bayan kasar Sin ta daidaita, da kyautata matakan kandagarkin annobar COVID-19, musamman ma a fannin manufar shige da fice.

A ranar 8 ga watan Janairu, wato ranar farko da Sin ta daidaita manufar shigowa kasar daga ketare, kididdigar da aka samu daga filin jirgin saman Yiwu ta bayyana cewa, yawan jiragen saman da suka tashi ko suka sauka a ranar ya yi daidai da na kafin bullowar cutar COVID-19.

Birnin Yiwu, wanda ya shahara wajen kasuwanci yana da alakar cinikayya tare da kasashe da yankuna guda 232, kuma jimillar cinikin waje na birnin ya zarce kaso 65 cikin dari bisa na jimillar GDPn nasa. Kafin bullowar annobar, yawan baki ’yan kasuwa dake zaune a birnin ya kai kimanin dubu 15, yayin da yawansu da ke zuwa birnin don kasuwanci ya zarce dubu 500 a duk shekara.

Amma sakamakon annobar da ake fama da ita a duk fadin duniya, yawan baki ’yan kasuwa da ke zaune a birnin ya ragu zuwa rabi. Bisa sabuwar kididdigar da hukumar kula da shige da fice ta ofishin ’yan sanda na birnin Yiwu ta bayar kwanan nan, an ce, ya zuwa yanzu, yawan baki ’yan kasuwa da ke zaune a birnin ya riga ya zarce dubu 10, kana jimillar tana ta karuwa.

Idan ana yawo a titunan da ke yankin kasuwanci a birnin Yiwu, za a iya gano cewa, a cikin wurin shan kofi da na nishadi, baki ’yan kasuwa masu tarin yawa suna sha, suna hira da abokan cinikinsu. Haka kuma, a ofishin tafiyar da harkokin shige da fice na birnin, ana iya ganin yadda ’yan kasuwa da dama da ke zuwa don gudanar da harkokin waje, kamar neman samun biza da dai sauransu.

Muhammad, dan kasar Jordan ne dake kula da wani kamfanin cinikin waje a birnin Yiwu, ya riga ya kafa matsuguni a birnin, bai koma garinsa ba a cikin wadannan shekarun baya da suka wuce. A ganin wasu ’yan kasuwa masu son sayen kayayyaki kirar Sin, Muhammad ya san komai game da Sin. Ya tabbatar da cewa, karin baki ’yan kasuwa za su dawo bayan lokacin hutu na bikin bazara na Sinawa, ganin yadda abokansa suke ta yi masa tambayoyi kan yanayin da Sin ke ciki. Ban da wannan kuma, ya ce, abokansa da dama, sun riga sun sayi tikitin jiragen sama don zuwan kasar Sin bayan bikin bazara. Hakan ya sa Mohammad yin imani sosai ga sabuwar shekara, ya ce, ya zuwa yanzu ya riga ya samu oda da darajarsu ta zarce Yuan miliyan 40, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 5.9.

Bugu da kari kuma, gwamnatin birnin Yiwu ta fara daukar matakai domin karfafa zukatan baki ’yan kasuwa dawowa birnin. A ranar 30 ga watan Disamban shekarar 2022, birnin Yiwu ya bayar da matakai goma ta fuskar ba da hidimomi, don kyautata muhallin kasuwancinsa, sa’an nan za a kaddamar da aiwatarwa a bana. Wadannan matakai sun kunshi fannonin ba da sauki ga baki wajen aiki da zama, da harkokin kasuwanci, da hidimar doka, da kafa unguwar kasa da kasa, da ba da aikin jinya ga baki, da karfafa zukatan mata baki wajen raya aiki, da bayar da labarai da dai sauransu, a kokarin daga matsayin ba da hidimomi ga baki, da kara kwarin gwiwar baki wajen yin kasuwanci da zuba jari a birnin Yiwu.

Kyautatuwar matakan kandagarkin cutar COVID-19 da kasar Sin ke aiwatarwa, ba kawai ya faranta ran baki ’yan kasuwa sosai ba ne, har ma ya karfafa zukatan ’yan kasuwa Sinawa dake birnin Yiwu.

Lu Rongqing, dan kasuwa ne dake sayar da kayayyakin wasan yara a birnin, ya kuma bayyana cewa, daga watan Disamban shekarar 2022, yawan oda ya karu a bayyane. Cikin ’yan kwanaki kawai, yawan odar da ya samu ya zarce na wata guda, wadanda darajarsu ta kai fiye da kudin Sin Yuan miliyan shida, kwatankwacin dalar Amurka dubu 885 a duk wata. Ya kara cewa, “bayan abokan cinikinmu sun dawo shagona sun gane wa idanunsu samfurin kayayyakin wasan yara, suna iya tabbatar da yawan kayayyakin da za su bukata, sai kuma tsara aikin samarwa yadda ya kamata. Lamarin da ya kara kwarin gwiwata sosai.”

Ban da Lu Rongqing, ayyukan kasuwancin sauran ’yan kasuwa su ma sun samu farfadowa. A cikin shagon Liu Junming, dan kasuwa mai sayar da kayayyakin wanka, wasu ma’aikatansa na fama da aikin tuntubar abokan cinikinsu da kwamfuta, yayin da wasu ke shirya shirin bidiyon kai tsaye, inda sukan yi amfani da harsuna daban daban wajen yin bayani kan sabbin manufofin shige da fice na kasar Sin, tare da ba da shawarwari kan zuwa kasar Sin. Liu Junming ya bayyana cewa, ko da yake yawan sabbin abokan cinikinsa yana ta karuwa a cikin wadannan shekarun da suka gabata, sakamakon raya kasuwanci a yanar gizo, amma a cikin abokan cinikinsa fiye da 1300, kaso 95 cikin dari bai hadu da su fuska da fuska ba. Yanzu, Liu Junming ya riga ya tattauna da yawancin abokan cinikinsa wajen haduwa da juna a birnin Yiwu bayan bikin bazara. Yayin da yake kokarin gayyato abokan cinikinsa, shi da tawagarsa suna kokarin kago sabbin kayayyaki. Liu ya ce, “tabbas ne za su yi mamaki da gamsuwa, bayan sun zo wurinmu.”

Kamar yadda Sinawa kan ce, tsuntsayen da ke tashi da sassafe na da abinci. Xu Xiaobao, dan kasuwar da ke sayar da kayayyakin ado a birnin Yiwu, a yanzu yana shirin zuwa lardin Guangdong da sauran wuraren kasar Sin don sayen na’urori da yin binciken kasuwa. A ganinsa, tabbas za a samu takara sosai bayan fara kasuwanci, bayan lokacin hutu na bikin bazara, don haka dole ne a tsara shiri tun da wuri, don share fage a fannonin tsara fasali da kayayyaki. Xu Xiaobao ya bayyana cewa, gaskiya ya gamu da matsala wajen kasuwancinsa a cikin shekaru biyu da suka gabata sakamakon cutar COVID-19.

A shekarar 2022, gwamnatin birnin Yiwu ta soke kudin hayar daki har na tsawon watanni shida ga dukkan ’yan kasuwa da ke cibiyar kasuwar Yiwu, lamarin da ya taimaka musu sosai. An ce yawan kudin hayar dakuna da aka soke gaba daya, ya wuce kudin Sin Yuan biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 147. Irin wannan taimako ya ba ’yan kasuwa kwarin gwiwar dagewa. Kaza lika an ce a shekarar 2022, yawan ’yan kasuwa dake ci gaba da gudanar da ayyukan kasuwanci a cibiyar ya kai kaso 87 bisa dari.

Otel-otel da dakunan sayar da abinci na birnin Yiwu, su ma suna jin farfadowar kasuwanci. Madam Xu Manlan, mai kula da wani dakin cin abincin kasar Nepal ta bayyana cewa, a jajiberin sabuwar shekarar 2023, wurinta cike yake da ’yan kasuwar gida da waje, sai dai ta kai har zuwa karfe 3 na daren ranar kafin tashi daga bakin aiki. Lamarin da ya sa ta yi imani sosai ga kasuwancinta a nan gaba.

Yanzu haka ana murnar bikin bazara a kasar Sin. A ganin Sinawa, lokacin bazara na alamta farfadowar rayuwa da fata. Sakamakon kyautatuwar manufofin kandagarkin cutar COVID-19, harkokin kasuwancin kasar Sin za su kara samun farfadowa, lamarin da zai kara azama ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar, wanda zai ci gaba da bayar da gudummawa ga karuwar tattalin arzikin duniya.

(Kande Gao daga sashen Hausa na CMG)


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Babban Shagon DuniyaCOVID-19KasuwanciSinZhejiang
ShareTweetSendShare
Previous Post

Benzema Ya Karya Tarihin Raul Gonzalez

Next Post

Da Dumi-Dumi: CBN Ya Kara Wa’adin Daina Amfani Da Tsoffin Kudade A Nijeriya

Related

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya
Daga Kasar Sin

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

3 months ago
Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin
Daga Kasar Sin

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

11 months ago
wang lili
Daga Kasar Sin

Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando

11 months ago
Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura
Daga Kasar Sin

Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura

1 year ago
Zambiya
Daga Kasar Sin

’Yar Kasar Zambiya: A Nan Kasar Sin, Ina Jin Tamkar Ina Gida!

1 year ago
Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
Daga Kasar Sin

Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin

1 year ago
Next Post
Da Dumi-Dumi: CBN Ya Kara Wa’adin Daina Amfani Da Tsoffin Kudade A Nijeriya

Da Dumi-Dumi: CBN Ya Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsoffin Kudade A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

June 7, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

June 7, 2025
Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

June 7, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

June 7, 2025
Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

June 7, 2025
COVID-19

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

June 7, 2025
Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

June 7, 2025
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023

Ana Ci Gaba Da Samun Rudani Yayin Da INEC Ta Jinkirta Rajistar Sabbin Jam’iyyu

June 7, 2025
Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan

Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan

June 7, 2025
Ban Sa Ran Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana Ba – Lamine Yamal

Ban Sa Ran Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana Ba – Lamine Yamal

June 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.