Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sake nanata ƙudirin sa na rage wa Gwamnatin Tarayya ƙarfin iko tare da sauya fasalin ƙasar nan idan ya ci zaɓe.
Haka kuma ya zargi jam’iyyar APC da ke mulki da cewar ta ƙi cika alƙawarin da ta yi na sauya fasalin ƙasar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi wannan maganar ne a dandalin wasa na Pa Oruta Ngele da ke Abakaliki, Jihar Ebonyi, lokacin da ya je can yaƙin neman zaɓe.
Atiku ya ce ‘yan ƙabilar Ibo sun sha yin kira da a sauya fasalin ƙasa (wato ‘restructuring’ a turance) domin su magance matsalolin da ke addabar yankin su, don haka ya ce sauya fasalin ƙasa na daga cikin manyan ƙudirorin da zai sa a gaba idan ya kafa gwamnati a matsayin shugaban Nijeriya.
Ya yi iƙirarin cewa ita APC ta gaza wajen cika alƙawarin da ta yi na sauya fasalin ƙasa, ya ce ya na kira ga al’ummar Ibo da ke Jihar Ebonyi da su yi watsi da jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa da za a yi.
Atiku ya samu babbar tarba a filin wasan inda ɗimbin jama’a su ka taru domin su saurare shi.
Ɗan takarar ya gode wa jama’ar jihar saboda goyon bayan da su ke ba PDP tun da aka kafa ta a cikin 1999.
Ya ce: “Na ƙudiri aniyar sakar wa matakan gwamnati da ke ƙasan Gwamnatin Tarayya ƙarfin iko da kuma sauya fasalin ƙasar nan; al’ummar yankin Kudu-maso-gabas sun daɗe su na ƙawazuci tare da yekuwar a sauya fasalin ƙasa saboda su na so su samu ƙarin ƙarfin iko da ƙarin kuɗi domin magance matsalolin da ke damun su.
“Mun amince da hakan kuma wannan ne ya sa hakan zai kasance wani babban ginshiƙi na gwamnatin mu. Saboda haka, ku ba mu goyon baya har ku ka ba mu damar zama shugaban ƙasa na gaba.”
Ya ƙara da cewa, “APC sun yi maku irin wannan alƙawarin. Shin amma sun yi? Sai su ka yi watsi da wannan batun na sauya fasalin ƙasa. Jam’iyyar su ta manyan ‘yan yaudara ce, kuma haɗakar su ta tantagaryar yaudara ce.
“Mun ƙudiri aniya kuma gaskiya ce mu ke faɗa, don haka idan ku ka ba mu goyon baya, za mu aiwatar da alƙawarin da mu ka ɗauka.”
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, zai kara da Atiku Abubakar na PDP a babban zaɓen da za a gudanar a ranar 25 ga Fabrairu.