Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce gwamnati za ta aiwatar matakan dunkulewa, da kara fadada karsashin farfadowar tattalin arziki, da ingiza farfado, da sayayya, da daidaita hada hadar cinikayyar waje da fannin zuba jari. Hakan dai na kunshe ne cikin kudurin da majalissar zartaswar kasar ta amincewa, yayin taron ta na jiya Asabar, wanda firaministan ya jagoranta.
Li, ya ce taron ya kuma amince da karfafa aiwatar da shawarwarin taron tsakiya, na tsara hada hadar tattalin arziki, da mayar da hankali ga tabbatar da daidaito a fannonin tattalin arzikin, da samar da guraben ayyukan yi, da daidaita farashi, ta yadda za a kiyaye gudanar fannonin tattalin arziki kan turba madaidaiciya.
Daga nan sai firaministan na Sin ya cewa, za a aiwatar da kwararan matakai, na tabbatar da aiwatar da manufofin daidaita tattalin arziki, da na bin bahasin ci gaban da ake samu. Har ila yau, za a gudanar da muhimman ayyuka, da daga matsayin kayayyakin aiki, da gyare-gyare karkashin tsarin kashe kudade, da manufofin hada hadar su, ta yadda hakan zai haifar da moriya ta zahiri.
Bugu da kari, Li Keqiang ya ce manufofin sun tanadi tsawaita wa’adin janye harajin VAT ga kananan masu biyan haraji, da samar da bashin gata ga masu mafi kankanta, da masu kananan sana’o’i. (Saminu Alhassan)