Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a yammacin ranar Lahadin da ta gabata ya kai yakin neman zabensa zuwa birnin Benin inda ya gudanar da wani taro da shugabannin siyasa, kwararrun kungiyoyin jama’a daga sassa daban-daban inda ya gabatar da kudurorinsa na shugabancin Nijeriya inda ya nemi ‘yan jihar da su zabi jam’iyyarsa APC a matakan siyasa baki daya a zaben da za a fara gudanarwa daga ranar 25 ga watan Fabrairu.
A fadar Oba na Benin inda mai martaba Oba Ewuare II tare da sarakunan gargajiya daga yankin Edo ta tsakiya da kuma Edo ta Arewa, Tinubu ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan amincewa da kara wa’adin daina amfani da tsoffin takardun naira da aka sauya wa fasali. Inda ya kara da cewa, yazo Birnin a makare sabida ya tsaya wurin rokon kara wa’adin daina amfani da kudin.
Tinubu ya ce wa sarkin “Kai Sarki ne mai karamci, na ga ka yi magana a kan rashin aikin yi na matasa, Mai Martaba Sarki, ka dogara da ni, ka albarkace ni, za mu nemo mafita kan samarwa matasanmu da aikin yi.
“Ka yi magana game da ilimin yaranmu, yana cikin shirye-shiryenmu kuma zan iya gaya muku kamar yadda nake tsaye a nan, shirin yana nan, gyaran ilimi zai tabbata.”
Ya ce, gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa, dukkan matatun mai da muke da su sun cigaba da aiki kuma bai kamata su bar wasu jam’iyyu kamar PDP ta yi mulki ba.