Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bada tabbacin aniyar gwamnatinsa na gudanar da sahihin zabe mai cike da gaskiya da adalci a 2023.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya rawaito cewa Buhari ha bayyana haka ne a fadar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a wata ziyarar ban girma da ya kai masa.
- Shugaban NIS Ya Sake Gargadin Marasa Gaskiya A Kan Harkokin Fasfo
- Jirgin Sama Kirar Kasar Sin Samfurin C919 Ya Tashi A Karon Farko Cikin Sabuwar Shekarar Zomo
Ya ce za a samar da daidaito wajen gudanar da sahihin zabe a kasar nan.
Ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta himmatu sosai wajen dorewa kan manyan ayyukan ci gaban da aka samu a karkashin jagorancinsa tsawon shekaru.
Ya ce babu wani tsarin dimokuradiyya da zai yi tasiri ba tare da yin kokari wajen taba kowane fanni na dan Adam ba.
Sai dai ya bayyana cewa, Masarautar Kano a tsawon shekaru, ta tashi tsaye wajen bayar da gudunmawarta ga ci gaban kasar nan.
Ya jaddada rawar da masarautun gargajiya ke takawa wajen bayar da lamuni ga neman shugabanci nagari a tsarin dimokuradiyya na gaskiya.
Da yake jawabi, Gwamna Abdullahi Ganduje, ya shaida wa Sarkin Kano cewa shugaba Buhari ya isa Kano ne domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatocin jihohi da na tarayya suka aiwatar.
A nasa jawabin, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce ya zama wajibi ‘yan siyasa masu yakin neman zabe su saurari korafe-korafen jama’a, domin sfahimtar juna.
Ya kuma jaddada bukatar gudanar da babban zaben cikin kwanciyar hankali da lumana, inda ya nuna cewa ‘yan siyasar da ke amfani da ‘uan daba wajen cin zabe za su kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
Ya yaba wa shugaba Buhari kan kara wa’adin canza tsofaffin kudade da CBN ya yi.