Hukumar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta ce, bangaren cinikayyar hidimomi a kasar ya samu tagomashi a bara, inda ya karu da kaso 12.9 cikin dari.
Alkaluman hukumar sun nuna cewa, jimilar darajar bangaren ya tsaya kan RMB yuan triliyan 5.98, kwatankwacin dala biliyan 884.29.
Cinikayya a bangaren hidimomin da suka shafi ilimi da kwarewar fasahohi, ta kai RMB yuan triliyan 2.51 a shekarar 2022, wanda ya karu da kaso 7.8. Adadin hidimomin da aka fitar a wannan bangare ma, ya karu da kaso 12.2 cikin dari zuwa RMB yuan triliyan 1.42, inda rukunonin kamar na sayen hakkin mallakar fasaha da hidimomin da suka shafi kumfyuta da na bayanai suke kan gaba a bangaren.
Bugu da kari, hidimomin da suka shafi tafiye-tafiye na ci gaba da farfadowa, yayin da cinikayya a bangaren ya karu zuwa kaso 8.4 bisa dari daga RMB Yuan biliyan 855 da ya kasance shekara guda da ta gabata. (Fa’iza Mustapha)