Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi, ta yi Allah wadai da kisan wani matashi dan shekara 20 da ake zargin wani hadimin tsaron tawagar dan takarar Gwamnan Jihar, Sadiq Baba Abubakar, ne ya aikata a kauyen Akuyam da ke cikin karamar hukumar Dambam.
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida a ranar Laraba, daraktan yakin zaben dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar PDP, Alhaji Faruk Mustapha ya nuna mamakinsa kan yadda za a bude wuta ga wadanda suka bayyana ra’ayinsu kan dan takara.
- Ina Ci Gaba Da Tattaunawa Da Kwankwaso Da Obi Kan Mara Min Baya – Atiku
- Emefiele Ya Bayyana A Gaban Majalisa Kan Sauya Fasalin Kudi
“Bai kamata kawai don mutane sun ce ba sa yi sai a bude musu wuta ba. Ya kamata idan ka na takara ka kwana da sanin wasu za su so ka wasu za su ki ka.”
Ya ce, harbin da jami’in tsaron tawagar dan takarar APC ya yi sam ba abu ne da ya dace ba, ya kara da cewa ya kamata a bai wa kowani mutum dama da ‘yancin zabin abun da yake so ba tare da musgunawa ba kamar yadda dokokin zabe suka tanadar.
Mustapha a daidai lokacin da yake tir da harbin mutum biyun, ya ce za su tabbatar da an yi adalci wajen nema ma wanda aka kashe adalci da kuma wanda aka jikkata.
DG din ya cigaba da cewa su a matakin PDP su na tafiyar da harkokin yakin zabensu ta hanyar bin dokoki da ka’idojin hukumar zabe domin tabbatar da an yi zaben cikin kwanciyar hankali.
Ya kara da cewa, “Mun kammala yakin zabenmu a kusan kananan hukumomi 14 cikin 20 babu inda ka ji an samu makamancin wannan matsalar. Don haka ya kamata sauran Jam’iyyu su yi koyi domin kare rayuka jama’a.”
Daga bisani ya yi kira ga ‘yan PDP da su tabbatar da sun kasance masu bin doka da oda a kowani lokaci.
Kazalika PDP din ta yi kira da a kaddamar da bincike na musamman domin tabbatar da hakikan abun da ya faru tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan lamarin.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin hukumar ‘yansandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ga ‘yan jarida ya shaida cewar, “Abun da ya faru shi ne a ranar Litinin da karfe 8:30pm dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar a lokacin da yake hanyarsa daga Dambam zuwa Akuyam domin yakin neman zabe, gab da shigarsu cikin Akuyam an kai farmaki ga tawagarsa.”
Kamar yadda yake cewa, bayan harin da aka kai wa tawagar dan takarar APC din, daya daga cikin masu tsaro a tawagar ya bude wuta inda ya samu mutum biyu masu suna Saleh Garba (Dan shekara 35) da kuma Yakubu Yunusa (Dan shekara 20) dukkaninsu mazauna kauyen Akuyam kuma an kaisu zuwa asibitin FMC da ke Azare domin kulawar Likitoci.
Ya kara da cewa, “A ranar Talata muka samu tabbacin cewa daya daga cikinsu ya mutu a lokacin da yake amsar kulawar Likitoci. Tunin kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, Aminu Alhassan ya bada umarnin a kaddamar da bincike kan lamarin. Ya yi addu’ar Allah ya jikan wanda ya rasu.”
A bangarensu kwamitin yakin zaben dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar, ya shaida cewar, ba su kai hari ga kowa ba illa ma su ne ‘yan adawarsu suka farmaka a kauyen Akuyam da ke karamar hukumar Dambam ya yin da suke cigaba da yakin zaben.
Da ya ke zantawa da manema labarai, daraktan yada labarai na kwamitin yakin zaben, Alhaji Salisu Barau, ya ce, duk da harin da aka kaddamar a kansu amma sun hana magoya bayansu maida martani domin kare rayuka da dukiya. Barau ya kara da cewa an lalata musu motoci a kalla 15 zuwa 20 gami da jikkata wasu daga cikin mutanensu.