A baya bayan nan, MDD ta fitar da rahoton dake kunshe da hasashen ci gaban da tattalin arzikin kasar Sin zai samu, na kaso 4.8 bisa dari a bana. Kaza lika wani rahoton na asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya nuna yadda tattalin arzikin kasar Sin zai daga, da hasashen karuwar kaso 5.2 bisa dari a shekarar nan ta 2023.
Game da hakan, yayin taron manema labarai na yau Laraba, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce karsashi da tasirin tattalin arzikin kasar Sin zai kara fadada a bana, kuma zai ci gaba da ingiza kwarin gwiwa, da karfin bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya.
Bugu da kari, yayin da take tsokaci game da kalaman babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO game da Sin, Mao Ning ta ce yankin Asia da Pacific ba fagen dagar gwada kwanjin siyasar shiyyoyi ba ne, kuma yankin ba ya maraba da fito na fito na masu tunanin cacar baka. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp