A ranar Laraba ne dai aka fara rade-radin cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na iya kara wa’adin makonni biyu kan zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu sabida kalubalen da suka dabaibaye hukumar na samar da kayan aiki.
Manya daga cikin wadannan kalubalen sun hada da yadda ake kona ofisoshin INEC a fadin kasar nan da kuma kalubalen rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas da Arewa maso Gabas.
Wani babban jami’in hukumar ya shaidawa jaridar Daily INDEPENDENT cewa duk da cewa, hukumar zabe ta kuduri aniyar tabbatar da ranar da aka tsara, amma al’amuran da ke faruwa baya-bayan nan a kasar nan na iya tilastawa hukumar ta sanar da karin wa’adin.
“Hukumar na yin duk mai yiwuwa domin ganin an gudanar da zabubbuka a lokacin da aka tsara tun farko, amma idan aka yi la’akari da dimbin kalubalen da ake fuskanta a fadin kasar nan, kamar kona ofisoshin hukumar, kalubalen tsaro da kai wa jami’an INEC hare-hare, da karancin mai tare da matsalolin da suka taso daga sauya fasalin kudi, ba zan yi mamaki ba idan an dage zaben da mafi karancin makonni biyu.”
Da aka tuntubi jami’in yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na INEC, Festus Okoye, ya musanta duk wani shirin kara wa’adin inda ya ce, ranakun da aka kayyade don gudanar da zaben na nan daram.