Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta kama wata mata mai suna Omoseyin Oluwadarasimi Esther wacce ke amfani da shafin Twitter mai suna @Simisola na Lala bisa laifin talla a shafin tana saida sabbin takardun kudi wadanda aka sauyawa fasali.
Kakakin hukumar ta ICPC, Azuka Ogugua, ya ce an kama ta ne sakamakon bayanan sirri da suka samu wanda ya sa jami’an ICPC suka gano tare da cafke wacce ake zargin cikin gaggawa.
ICPC ta ce Oluwadarasimi, ‘yar kasuwa ce mai sana’ar kula da fatar jiki, sayar da man fetur, harkokin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da sauran sana’o’i, ta yi amfani da damar karancin sabbin kudin inda ta fito fili tana tallata sayar da sabbin takardun kudin ta shafinta na manhajar Twitter.
“Ana zargin cewa, tana hada baki da wasu batagarin ma’aikatan banki suna karkatar da sabbin takardun kudi daga bankunan zuwa ‘kasuwannin badakala’.”