Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin a gaggauta cafko mata tare da gurfanar da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas bisa zarginsa da barazana ga rayuwar mutane, kokarin kawo rudani ga zaman lafiya da kuma kalaman nuna kiyayya.
Mai shigar da karar, Mahmoud Lamido, ta bakin lauyansa, Bashir Yusuf Muhammad Tudun wazirchi, ya nemi a kama Abbas bisa zarginsa da yi masa barazana ta wayar tarho, inda ya ce zai kashe shi.
Mai shari’a S.A. Amobeda ta bayar da umarnin cafko mata shi sannan ta dage sauraron karar har zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu domin gabatar da rahoton cikakken bin umurninta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp