Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci kan matakin da shugaban jam’iyyar Stram Kurs ta kasar Denmark ya dauka a baya-bayan nan, na kona Alkur’ani a kusa da ofishin jakadancin Turkiye a kasar Sweden.
Mao Ning, ta yi tsokacin ne yayin taron manema labarai na yau Alhamis, tana mai cewa, ya kamata a rika girmama ra’ayi da akidun mabiya addinin musulunci.
Haka kuma, kakakin ta tabo batun ziyarar sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO a Korea ta Kudu da Japan, inda ta ce da gangan ya ambato batun “barazanar kasar Sin” domin lalata dangantaka a yankin, tana mai cewa, yunkurin na sa abun damuwa ne matuka.
Game da kame kayayyakin gorar ruwa da suka fito daga jihar Xinjiang ta Sin da Amurka ta yi bisa dogaro da abun da take kira da “tilasta kwadago”, Mao Ning ta bukaci Amurka ta daina kokarin danne masana’antun kasar Sin ba tare da dalili ba. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)