Hukumar kula da aikin hajji ta kasa, ta sanar da rarraba kujerun aikin hajjin bana ga jihohi 36 har da babban birnin tarayya Abuja da jami’an tsaro a karshen zamanta da ta yi da mahukunta Hukumar inda ta tabbatar da rarraba kujerun.
Kujerun ga su kamar haka:
- Abia 53
- Adamawa. 2669
- Anambra. 39
- Bauchi. 3, 132
- Bayelsa. 35
- Benue. 236
- Borno. 2,735
- Cross Rivers. 66
- Delta. 74
- Nassarawa. 1,567
- Niger. 5,165
- Ogun. 1,139
- Ondo. 436
- Osun. 1,054
- Oyo. 1,441
- Yobe. 1,968
- Ebony. 117
- Edo. 274
- Ekiti. 197
- Enugu. 40
- FCT. 3,520
- Gombe. 2,301
- Imo. 30
- Jigawa. 1,525
- Kaduna. 5,982
- Kano. 5,902
- Katsina. 4,913
- Armed Forces : 548
- Kebbi. 4871
- Kwara. 3,219
- Lagos. 3,576
- Plateau. 1,984
- Rivers. 50
- Sokoto. 5,504
- Taraba. 1,590
- Zamfara. 3,083
Za a bayyana adadin kujerun jihar Kogi da zarar an kammala duba tsare-tsare hukumar jihar yayin da aka dakatar da jihar Akwa Ibom sabida rashin sabunta lasisinta.
Ana sa ran dukkan jihohin za su mika wa Hukumar kashi 50 cikin 100 na kudin kujerun kafin ranar 10 ga watan Fabrairu. Duk jihar da ta gaza bayar da kudinta acikin wannan wa’adin, za a rage mata yawan kujerun da aka tanadar mata.