• English
  • Business News
Sunday, May 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Afirka Ba Ta Bukatar Lakca

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Afirka Ba Ta Bukatar Lakca
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen, ta ziyarci kasashen Afirka da suka hada da Senegal, da Zambia, da Afirka ta kudu a kwanan baya, wadda kamar yadda sauran manyan jami’an kasar suka saba yi, ita ma ta zargi kasar Sin da haifar da matsalar bashi ga Zambia da sauran kasashen Afirka.

Sai dai alkaluma ba sa karya. Wani rahoton da cibiyar nazari ta “Debt Justice” ta kasar Birtaniya ta fitar a kwanan baya ya yi nuni da cewa, bisa ga kididdigar da Bankin Duniya ya yi, daga cikin basussukan da gwamnatocin kasashen Afirka suka ci, kaso 12% na kasar Sin ne, a yayin da kasashen yamma, musamman ma sassa masu zaman kansu na kasashen yamma suke binsu kaso 35%. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta samar da basussuka ne kan kudin ruwan da bai wuce kaso 2.7% ba a duk shekara, a yayin da kudin ruwan da kasashen yamma suke karba ya kai kaso 5% a duk shekara. In mun dauki kasar Zambia ga misali, wadda bisa ga alkaluman da ma’aikatar kudi ta kasar ta samar, an ce, daga cikin basussukan da kasar ta karba, kaso 24% ne hukumomin kudi mallakar bangarori da dama suke binta, a yayin da kasashen yamma suke binta kaso 46%.

Ban da haka kuma, Sin da kasashen yamma sun sha bamban sosai, duk da cewa dukkansu na bin kasashen Afirka basussuka. Na farko, burin da suke neman cimmawa ba iri daya ba ne. Kasar Sin na ganin cewa, ainihin matsalar basussukan da Afirka ke fuskanta ita ce matsalar bunkasuwa, don haka, ta fi mai da hankali a kan tabbatar da dauwamammen ci gaban kasashen Afirka, a yayin da take samar musu basussuka, matakin da ya sa ta fi samar da basussuka a fannonin kere-kere, da ma manyan ababen more rayuwa, wadanda suka kyautata bunkasuwar tattalin arziki da rayuwar al’ummar kasashen. Misali a kasar Zambia, tashar samar da wutar lantarki da karfin ruwa da kasar Sin ta samar da kudaden jarinta, da ma gina ta tuni ta fara aiki, wadda ke iya samar da wutar da ta kai MW750, wadda ta taimaka ga rage fitar da iskar Carbon da ton dubu 663.5 a kowace shekara, baya ga kuma yadda take taka muhimmiyar rawa wurin bunkasa tattalin arziki. A sa’i daya kuma, kasashen yamma sun kasa sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin Afirka, har ma sun sa su kara shiga kangin talauci, kuma da hakan suke ta kara neman basussuka daga wajensu. Na biyu kuma, kasar Sin na aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka ne bisa daidaito, ba tare da tsoma baki cikin harkokin gidansu ba, don haka ma, ba ta taba gindaya sharudan siyasa a yayin da take bin su basussuka ba, sabanin yadda kasashen yamma su kan gindaya sharudan siyasa, da suka shafi hakkin bil Adam, da gyare-gyaren dokoki da makamatansu, a yunkurin tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen bisa ga basussukan da suka samar. Na uku, kullum kasar Sin na dora muhimmanci a kan saukaka wa kasashen Afirka matsalar basussuka, ganin yadda take kokarin shiga hadin gwiwar sassa daban daban kan batun bashi, har ma ta zamanto kasar da ta fi yawan basussukan da ta tsawaita wa’adin biyansu daga cikin kasashen G20, sabanin yadda kasashen yamma suka yi shiru game da batun tsawaita wa’adin basussukan nasu sassa masu zaman kansu ke bin kasashe mafiya fama da talauci, baya ga kuma yadda suke yayata zancen wai “tarkon bashin kasar Sin” .

Da haka muna iya gano cewa, maganar wai “tarkon bashin kasar Sin”, tarko ne kasashen yamma suka kafa don lalata hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, wanda kuma kasashen Afirka suka yi watsi da shi. Mista Emmanuel Mwamba, tsohon jakadan kasar Zambia a kungiyar tarayyar Afirka ya bayyana cewa, bai dace jami’ar Amurka ta furta kalamai masu nasaba da alakar Sin da Zambia, yayin da take ziyarar aiki a Zambia ba, domin da farko ma hakan ya sabawa da’ar ayyukan diflomasiyya, baya ga kuma yadda kamfanonin kasar Sin suka dukufa a kan gina manyan ayyuka, da suka hada da tashar samar da wutar lantarki, ya taimaka matuka ga bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma a kasar ta Zambia.

Akwai dimbin matsalolin da kasashen Afirka ke fuskanta, kuma ba a rasa damammaki ga wadanda da gaske ne suke son taimaka wa kasashen Afirka. Wanda ke son taimaka wa kasashen Afirka daidaita matsalar basussuka, ya kamata ya dauki hakikanin matakai. Kasashen Afirka ba su bukatar lakca, kuma bai dace Amurka ta raina ’yancinsu na zabar abin da suka ga ya dace ba. (Mai zane: Mustapha Bulama)

Labarai Masu Nasaba

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Manoman Kwakwa 50 Sun Samu Horo Kan Noman Zamani

Next Post

Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Da Aka Yi Wa ‘Yan Banga A Katsina

Related

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara
Daga Birnin Sin

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

12 hours ago
An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva
Daga Birnin Sin

An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

13 hours ago
Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu
Daga Birnin Sin

Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

15 hours ago
Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali
Daga Birnin Sin

Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

17 hours ago
Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow

18 hours ago
Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo
Daga Birnin Sin

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

1 day ago
Next Post
Tashoshin Talabijin 6 Zasu Haska Shiri Na Musanman Kan Rayuwar Shugaba Buhari

Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Da Aka Yi Wa 'Yan Banga A Katsina

LABARAI MASU NASABA

Barin Liverpool Ita Ce Shawara Mafi Wahala Da Na Taɓa Yankewa A Rayuwata -Alexander 

Barin Liverpool Ita Ce Shawara Mafi Wahala Da Na Taɓa Yankewa A Rayuwata -Alexander 

May 11, 2025
Shugaban NPA Ya Sha Yabo Kan Yadda Ya Bunƙasa Tashar Jiragen Ruwa Ta Onne

Shugaban NPA Ya Sha Yabo Kan Yadda Ya Bunƙasa Tashar Jiragen Ruwa Ta Onne

May 11, 2025
Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)

Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)

May 11, 2025
Kaduna Ta Gano Ma’adanai 73, Yayin Da Take Neman Masu Zuba Jari

Kaduna Ta Gano Ma’adanai 73, Yayin Da Take Neman Masu Zuba Jari

May 11, 2025
Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

May 10, 2025
An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

May 10, 2025
Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

May 10, 2025

Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Ba Dalibai 164 Tallafin Karatu

May 10, 2025
Dalilan Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmaci (5)

Dalilan Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmaci (5)

May 10, 2025
Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

May 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.