Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa ‘yan sa-kai a dajin Yargoje da ke cikin ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
BBC ta rawaito cewa, wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Malam Garba Shehu, ya fitar ya ce harin wanda ‘yan bindiga suka kai ya yi sanadin mutuwar ‘yan sa- kan da dama.
- Tinubu Yana Kaunar Nijeriya, Ku Zabe Shi – Buhari Ga ‘Yan Nijeriya
- Gwamnonin APC Sun Gana Da Buhari Kan Bukatar Cire Wa’adin Karbar Tsofaffin Kudi
‘Yan bindigar sun yi wa ‘yan sa-kan kwanton ɓauta a dajin a lokacin da suke ƙoƙarin ƙwato wasu shanu da aka sace.
Shugaban ƙasar ya bayyana alhininsa kan rasuwar jami’an sa-kan tare da jajanta wa iyalansu, yana mai cewa Nijeriya ba za ta manta da sadaukarwar da suka yi na kare ƙasa, tare da yaƙar miyagun laifuka a ƙasarsu ba.
“Muna addu’a tare da jajanta wa iyalan mamatan a wannan lokaci na alhini. Muna addu’ar Allah ya gafarta musu” in ji Buhari.
Jihar Katsina da sauran jihohin arewa maso yammacin ƙasar na fama da matsalolin ayyukan ‘yan bindiga, waɗanda ke yawan kai hare-hare, tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.