‘Yan bindiga sun sako mutum 2 da suka sace a Cocin Prelate, Methodist Church of Nigeria, da suka hada da Emence Samuel Kanu Uche, da wasu Jami’an cocin biyu, wadanda aka sace ranar Lahadin data gabata.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Abiya, Mista Geoffrey Ogbonna, ne ya bayyana hakan ga LEADERSHIP da misalin karfe 9:40 na daren ranar Litinin.
Sufetan ‘yan sandan ya shaida wa wakilinmu cewa, “Shugaban da wasu mutane biyu sun samu ‘yancinsu.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba ne suka yi garkuwa da mai suna Methodist na gida mai lamba daya da ke kan titin Ihube-Okigwe-Umunneochi kan babbar hanyar Fatakwal zuwa Enugu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp