A yayin taron manema labaru da aka saba gudanarwa, a ranar Litinin 6 ga wata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta amsa tambayar da aka yi mata game da hadin kan kasashen BRICS, inda jami’ar ta ce bayan gwagwarmaya da aiki tukuru da aka yi na tsawon shekaru fiye da goma, hadin gwiwar BRICS ya nuna kyakkyawan halin ci gaba mai karfi, wanda hakan ya sa kungiyar ta kasance muhimmin karfi a harkokin kasa da kasa.
Mao Ning ta ce a matsayinta na shugabar BRICS a shekarar da ta gabata, kasar Sin ta samu nasarar karbar bakuncin taron kolin kungiyar karo na 14, tare da samun jerin nasarori masu inganci, da ba a taba ganin irinsu ba.
Mao Ning ta kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye ruhin BRICS na bude kofa, da hakuri da juna, da samun nasara tare ta hanyar hadin gwiwa, don yin kokari tare da abokanta kasashen BRICS, wajen karfafa hadin gwiwa tare da sauran kasuwanni da kasashe masu tasowa, kana da inganta fadada kungiyar ta BRICS bisa tushen gudanar da cikakkun tattaunawa, da cimma ra’ayi daya bayan gudanar da shawarwari. (Mai fassara: Bilkisu Xin)