Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya shaida wa Shugaban Hukumar Zaɓe na Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, cewa sauya launin kuɗi ba zai shafi zaɓen 2023 ba.
Ya ce CBN zai samar wa INEC da dukkan kuɗaɗen da hukumar ke buƙata a lokacin zaɓuɓɓukan ranar 25 ga Fabrairu da na 11 ga Maris, 2023.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele, ya shaida wa Yakubu cewa a ko da yaushe CBN na goyon bayan INEC ta kowane fanni domin tabbatar da cewa ta gudanar da aikin da aka ɗora wa hukumar a cikin nasara.
Ya ce: “Mu na shiga harkokin ayyukan INEC adanawa da ajiyar kayan zaɓe, har ma da amfani da motocin CBN masu sulke wajen rarraba kayan zaɓe.
“Mu na farin cikin cewa a cikin wannan kyakkyawar alaƙa tsakanin CBN da INEC, ba mu taɓa kawo wa INEC cikas ko dagula masu lissafi ba. Saboda haka ɗin ne ma ba ku gudun mu, ga shi a yanzu ma kun dawo mana a wannan zaɓen.
“Idan shugaban INEC zai tuna, lokacin da na kai maka ziyara a baya, ka tambayi yadda CBN zai samar wa INEC kuɗaɗen waje domin sayen na’urar tantance masu rajistar zaɓe (BVAS), da sauran kayan aikin zaɓe. Na ba ka tabbacin za a samar, kuma an samar ɗin.
“Saboda haka, CBN ba zai bari a yi amfani da shi ba wajen kawo wa zaɓen 2023 cikas.
“Don haka ina tabbatar maka idan ka na buƙatar takardun kuɗaɗe domin biyan motocin sufuri kuɗin su a hannu, bayan ka yi biya ta tiransifa, to CBN a shirye ya ke ya bayar.”
Tun da farko, Farfesa Yakubu ya nemi haɗin kan CBN domin tabbatar da zaɓen 2023 cikin nasara, musamman ganin yadda ake ta haƙilon ƙarancin kuɗaɗe kusa da zaɓe.
Ya ce INEC ta yi shiri tsaf domin tabbatar da zaɓen 2023 ya zama sahihin zaɓen da a tarihi ba a taɓa yin kamar sa ba a Nijeriya.