Kungiyar Ibo (Igbo), mai suna “Kaduna State Igbo Community Welfare Association”, ta nuna goyon bayanta ga dan takarar gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani na Jam’iyyar APC.
Da ya ke magana a wurin wani taro ranar Lahadi a Kaduna, mai bada shawara na kungiyar, Valentine Ewuzie, ya ce, “Uba Sani, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, shi ne ya cancanta da ya rike ofishin gwamnan Jihar Kaduna.”
Ewuzie ya ce, Sanata Uba Sani ya nuna ya kaunar al’ummar Ibo (Igbo).
Ya kuma kara da cewa, “Mun yi nazari da tantance dukkan ‘yan takarkarun, kuma mu na ji yanzu, ba tare da gutsutstsura kalamai ba, mun tabbatar kai ne dan takarar mu.” Inji shi.
“Kuma kasancewa mafi tsari, za mu iyakacin kokarin mu, don ganin ka zama gwamnan jihar Kaduna.”
Ya kuma tuna lokacin da Uba Sani ya ke mai ba da shawara ga gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’i, ya zauna da kungiyar Ibo na jihar, ya kuma tabbar da amincin sa. Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna na soke bambanci wurin daukar kwararru a aiki, har da malamai a kan cancanta.