Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gana da shugabannin kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) da gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, a fadar gwamnati da ke Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya rahoto cewa tun da farko shugaban kasa ya shirya ganawa da daukacin mambobin kungiyar gwamnonin kafin daga baya aka fasa shirin.
Mahalarta taron sun hada da shugaban NGF, Aminu Tambuwal, Gwamna Atiku Bagudu da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasa ya yi wata ganawar sirri da gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC inda ya bukaci ‘yan Nijeriya da su ba shi kwanaki bakwai don magance kalubalen da ya dabaibaye batun ranar daina amfani da tsoffin takardun kudi wanda babban bankin kasa (CBN) ya bullo da shi.