A kwanakin baya, hukumomin duniya daban daban, sun daga hasashen bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin.
A halin yanzu, dukkanin sassan kasar Sin na kokarin raya tattalin arziki, don samun farfadowar fannin.
Asusun ba da lamuni na duniya IMF, da sauran cibiyoyin hada hadar kudade na duniya, sun daga hasashensu game da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin.
A bangarensa asusun IMF ya ba da labari a jiya cewa, bayan da aka soke matakan killace jama’a domin cutar COVID-19 a kasar Sin, an samu karuwar zirga-zirgar mutane da ayyukan tattalin arziki. Kuma a bana tattalin arzikin kasar Sin zai samu karuwa, wanda zai ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya.
Wakilin kungiyar hadin gwiwa da bunkasa tattalin arziki dake kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana da babbar kasuwa, kana ta kiyaye sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje, da yin hadin gwiwa tare da sassan kasa da kasa.
Kaza lika kasashen duniya suna fatan tattalin arzikin Sin zai samar da karfin bunkasa ci gaba a duniya. A lokaci guda, bunkasuwar tattalin arzikin Sin za ta taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin duniya da na yankuna. (Zainab)