Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ranar Laraba da rana ya sauka a Filin Jirgin Saman jihar Yobe da ke Damaturu (Muhammadu Buhari International Cargo Airport) wanda ya samu gagarumar tarbar manyan jiga-jigan yan siyasa a jihar da na kasa baki daya.
Dan takarar shugaban kasa, zai fara da kai ziyarar ban-girma a Fadar shugaban Majalisar Sarakunan jihar Yobe, Mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Ibn Abali dake Potiskum kafin ya zarce filin wasa na 27 August inda zai gudanar da taron yakin neman zaben sa a Damaturu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp