An ruwaito cewa, wani Balaraben kauye ya zo wurin Annabi ((SAW)) yana neman wani abu, sai Annabi ((SAW)) ya ba shi abin da ya samu a wannan lokaci, sannan Annabi ((SAW)) ya yi masa wasan kakaci da cewa “Na Kyautata maka ya kai Balaraben kauye?”, sai ya ce, “Ina sam baka kyautata min”, sai Sahabbai ransu ya baci suka yi fushi, suka tashi suna nufin farmasa, sai Annabi ((SAW)) ya yi ishara gare su, su kyale shi, sai Annabi ((SAW)) ya tashi ya shiga cikin gida ya kara nemo wani abu ya ba shi sannan ya sake tambayarshi “Na Kyautata maka ya kai Balaraben kauye?”, sai ya ce “Na’am lallai ka kyautata min yanzun, Allah ya saka maka ya dan’uwana da alkhairi”. Sai Annabi ((SAW)) ya ce masa, “ka fada wani abu wanda ya bata wa Sahabbaina rai, ina so ka sake fadar addu’ar da ka yi min a gabansu, sabida abinda ke cikin zuciyoyinsu a gare ka ya fita”. Sai ya ce, zan fada musu.
Wata rana, da Balaraben ya dawo wurin Annabi (SAW) yayin da yake zaune cikin sahabbansa, sai Annabi (SAW) ya ce, wannan Balaraben nan ya zo, mun bashi kyauta sai ya nemi a kara masa, bayan mun kara masa sai ya raya a zuciyarsa cewa, abin da aka kara masa ya wadatar da shi, Balarabe haka aka yi? Annabi ya tambaye shi, sai ya amsa da cewa, Na’am Ya Rasulallahi haka aka yi, Allah ya saka maka, ka zama dan’uwa. Sai Annabi (SAW) ya ce misalina da wannan Balaraben kamar wani mutum ne da yake da Rakuma ta tsinke ta yi Daji, sai mutane suka bi ta a guje suna son su kamo ta, sai ya zama wannan bin da suke yi mata ba ya kara mata komai sai gudu, da mai rakumin ya ga ya kusa asarar rakumarsa, sai ya kira masu bin ta, ya ce su dawo su kyale ta, na san yadda zan yi in kama rakumata. Sai Mutumin ya shiga gabanta, ya tsugunna kamar ya dibo mata abinci, sai Taguwar ta zo ta tsugunna a gare shi.
Annabi (SAW) ya ce, da na kyale ku lokacin da Balaraben nan ya fada wannan maganar kun far masa kun kashe shi da sai ya shiga wuta, amma yanzun zai mutu da Imani ya shiga Aljannah.
An yi wani Malami mai kudi (Mai Littafin Risala) da shi da wani waliyyi masanin Alkur’ani har yana tasarrufi da Alkur’ani, Zaki ne abin hawanshi, macijiya ce bulalar da yake dukan Zakin da ita, wata rana sai ya ji labarin wannan Malami mai kudi kuma masanin Alkur’ani ne, sai ya kawo masa ziyara don samun Ilimi cikin Alkur’ani. Ya tambaya ina Malam yake, sai aka ce yana gidan Sarki, sai ya ga wata Mace tana shara a Masallaci, ya tambaya wacece wannan, aka ce masa Mahaifiyar Malam ce, sai ya raya a zuciyarsa cewa wannan Malamin dan Duniya ne kawai, yana gidan Sarki kuma Mahaifiyarsa ce ke share masa masallaci, yana jiran Malam, sai ga Malam ya iso a kan doki wani tsoho ya rike masa linzami ya sauka, sai yace wannan tsohon kuma wane ne, sai aka ce masa mahaifin Malam ne, kawai sai ya yi fushi ya juya ya wuce, bayan ya koma wurin zakinsa zai hau, sai Zakin ya bude baki yana nufin far masa, sai ya fahimci cewa, lallai akwai wata Magana, sai ya yi hakuri ya koma har suka hadu da Malam, ya bayyana masa irin abubuwan da suka faru da shi bayan ya yi fushi ya wuce.
Sai Malam ya bayyana masa cewa, yana zuwa fada ne sabida Sarkin Garin ba ya adalci sai in ya gan shi, shi kuma sai ya daura wa kansa kullum sai yaje,” Sarkin ba ya so ya gan ni ni kuma dole sai na je”. Sharar Masallaci kuma, Hadisin Annabi (SAW) ne wanda yake cewa, Duk mai sharar Masallaci, Wuta ba za ta ci wannan jiki ba, ni kuma sai na yi kwadayin Allah ya tseratar da Mahaifiyata zuwa Aljannah. Batun galan-galan na Giya kuma da ake shiga da su gidana, na yi wa’azi jama’a su daina shan giya sun ki, ni kuma ina da kudi, sai na yanke shawarar saye giyar garin baki daya, sai na haka rami a cikin gidana, nake zubarwa.
Batun mahaifina na rike min linzamin doki in zan hau ko kuma in zan sauka, a Hadisin Annabi (SAW), ya ce, duk mai rike wa Malami Linzamin Dabba, wuta ba za ta ci shi ba, ni kuma sai na zabi Mahaifina a kan wannan Daraja.
Sai malamin Alkur’ani ya ce, na Fahimta, Littafin Risala na ji Labari na zo nema, sai ya ce masa, ta fi zan turo maka. A ruwa ya jefa littafin har ya isa garin Malam Mai Alkur’ani.
An ruwaito daga Annabi (SAW) yana cewa “Kar wani daga cikinku ya isar min a kan sahabbaina, kar wani ya zo ya gaya min laifin wani daga cikin sahabbaina, ina so in dinga fitowa zuwa gare ku, babu bacin rai da kowa a cikin kirjina” sai dai abin da zai cuci Jama’a dole a fada.
Yana daga tausayin Annabi (SAW) a kan Al’ummarsa, tausaya da saukakawarsa a gare su. Da yawa ya ki wasu abubuwa tsoron kar a wajabta wa al’ummarsa wannan abin, kamar fadinsa inda yake cewa “Ba don kar in tsananta wa al’ummata ba, da na umarce su da yin Asiwaki (ko makilin) duk yayin Alwala”. Akwai kuma lamarin Sallar dare ta watan Ramadana. Watan Ramadana ya kama, wata rana sai Annabi (SAW) ya shigo masallaci da daddare ya kabbara Sallah, wadanda suke cikin Masallacin, sai suka bi shi Jam’i aka yi Tarawihi, da safe sai suka bawa abokanansu labarin Sallar, da dare ya yi, sai Masallaci ya cika, Annabi (SAW) ya yi Sallar Tarawihi da su, wani daren, Labari ya yadu duk Birni da Kauye, Sahabbai ta ko’ina sun cika Masallaci, sai Annabi (SAW) ya ki fitowa wannan daren, Bayan Safiya ta yi, sai wasu daga cikin sahabbai suka ce, Ya Rasulallahi, jiya Masallaci ya cika sosai muna ta jira ka fito ka yi mana sallah, Annabi (SAW) yace “Da na fito da an wajabta muku wannan Sallar.”
Yana daga cikin tausayawa da saukakawa al’ummarsa, haninsa da jera Azumi biyu a jere ba shan ruwa amma shi yana yin sama da biyu.
Da kinsa ga shiga Ka’aba a aikin hajji, sabida kar kowane Alhaji ya ce dole sai ya shiga Ka’aba in ya je aikin Hajji. A ranar Fat’hu Makkah, bayan ya fito Ka’aba sai aka ga ransa a bace, bayan an tambaye shi me ya sa? Sai ya ce, kar Al’ummata ta raya dole sai ta shiga Ka’aba in ta yi aikin Hajji, wannan Sunnata ce kawai. Sayyada A’isha ta ce masa, Ya Rasulallahi ni ma ina son in shiga Ka’aba, sai yace mata, bari dare ya yi, bayan ya dauko ta a daren, sai ya shigar da ita Hijru Isma’ila ya ce nan ma, a da Ka’aba ne.
Annabi (SAW) ya roka wurin Ubangiji cewa, duk wanda ya bata masa rai har ya yi masa tir, Allah ya maida wannan ya zama shiriyarsa da rahama a gare shi.
Annabi (SAW) ya kasance in yana Sallah ya ji kukan yaro, sai ya yi gaggawa wurin takaita Sallar. Yayin da mutanen Annabi (SAW) suka karyata shi, Mala’ika Jibrilu ya zo masa, ya ce, Ubangijinka ya umarci Mala’ika mai kula da Duwatsu ya yi maka duk abin da ka umurce shi, sannan Mala’ikan ya yi Sallama ga Annabi (SAW) ya ce, ya Annabin Allah ba ni umarnin yadda kake so in hallaka su, sai Annabi (SAW) ya ce masa, ina kwadayi a tsatsonsu a samu wanda zai bi ni da gaskiya.