Barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, Shafin da ke zakulo muku batutuwa da suka shafi al’umma, wanda ya hadar da zamantakewa na rayuwar yau da kullum, zamantakewar aure, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da kallon da wasu samarin ke yi wa mafi yawan ‘Yan mata a yanzu, musamman yadda rayuwar ta zo a zamanance da kuma wayewa. Da yawan samari a yanzu na yi wa mafi yawan ‘Yan mata kallon zawarawa (Lalatattu masu bin maza), wanda dalilin hakan ke sa mafi yawan ‘Yan mata damuwa sakamakon rashin yi masu aure da wuri ko kuma rashin samun tsayayye da wuri.
A cewar wasu ‘yan matan, a duk lokacin da za su fita daga gida mafi yawan maza na yi masu kallon masu fita yawon banza zuwa wajen samari, wanda hakan kuma ba daidai ba ne. Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin matasa game da wannan batun; Ko me yake janyo hakan?,
Shin laifin waye tsakanin ‘Yan matan da Samarin?, Ta wacce hanya za a magance wannan matsalar?, Inda suka bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
Teemah Dimple daga Jihar Kano:
Duk saurayin da yake wa ‘yan mata kallon zawarawa toh! gaskiya shi ma ba mutumin kwarai ba ne. Ma’ana yana cikin masu lalata matan ne, idan ba haka ba ba zai taba irin wannan tunanin ba idan shi mutumin kirki ne, saboda mutanen kirki ana samunsu da kyautata wa mutane zato, sannan ba zai yi tunanin wani yana yin abun da shi baya yi ba.
Kowa yana da laifi, ba zan ce samari ne kadai da laifi ba ko ‘yan mata ba. Kuma a duka za a ce laifin yana zama kusan 50/50 ne ‘cos in the first place’ bai kamata namiji ya nemi mace da fasikanci ba saboda Allah (SWT) ya haramta zina, ya ce; Kar a kusanci zina ba ma aikatawar ba, duk wani abu da zai yi leading to zina yace a kaurace masa, haka Manzan Allah (SAW) ya ce zina bashi ce, duk wanda yayi da ‘yar wani za a yi da tashi, likewise idan yayi da ‘sister or mother’ din wasu (and so on) shi ma sai an yi da nashi. Saboda haka duk namijin da ya san mai yake yi mai cikakken hankali da tunani ba zai taba sha’awar aikata hakan da wata macen da ba matar shi ba. And laifin mata kuma shi ne; na daya kwadayi da son abun duniya shi yake rufe musu ido ya sa su amince da bukatar wani fasiki idan ya zo musu da ita, wasu kuma saboda soyayya ta rufe musu ido sun gwammace su sabawa ma Mahaliccinsu saboda farin cikin wani kato, duk da sunan suna tsoron rasa shi, wanda duk hakan ba dai-dai bane.
Mace an san ta da kunya da kamewa, duk da musulunci bai ce mace ce kawai za ta kame ba har da mazan. Amma bai kamata su yi biyayya ga abun halitta ba wurin sabawa mahaliccinsu. Ina kunya da kamewar su yake? Me ya sa idan namiji ya zo da irin bukatar banza ba za su yi baran-baran da shi ba? ‘Cos’ Hausawa suna cewa sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga. Me ya sa ba za su zamo masu sitirce jikinsu ba, kamar yadda Allah yayi mana umarni a cikin Alkurani ba? Me yasa ba za su ringa tuna ‘consekuences’ da aikata fasikanci zai haifar ba? Har ‘ya’ya da jikoki? Me ya sa ba za su tuna azabar Allah da ya tanadar wa masu aikata irin wannan laifin ba? Me yasa ba za su gane mutuncinsu shi ne kimar su da darajar su ba? Me yasa ba za su gane cewa ZINA tana bin jini ba?.
Sunana Mansur Usman Sufi (Sarkin Marubutan Yaki) Jihar Kano Nijeriya:
Batu na gaskiya hakan na faruwa ne duba da yadda al’umma ta baci, musamman ‘ya’ya mata, ko da ace mace ba ta bawa wani saurayi kanta ba, za ka samu ko tana biye-biyen mata, kuma duba da yadda zina ta zama ado kuma ba komai ba shi yasa zargin ya yi yawa, Amma wani hanzari ba gudu ba, duk saurayin da ka ga yana zargin budurwar sa da lalata to bai je ya nemi ta gari ba, sai ya tafi wajen mai kyale-kyale. Amma shi a kansa ya san indai zai je ya nemi auren macen da ba zai zarge ta ba. Sannan duk saurayin da yake ganin kowacce mace lalatacciya ce to shi ma yana lalata ‘ya’yan wasu ne ko yana tare da masu aikatawa, amma idan ya zamto mutumin kirki ba zai taba kawo hakan a ransa ba. Samari ke da laifi akan wannan maudu’i, hanya mafi saukin magance ta ita ce; a kiyaye zargi a dinga yi wa juna kallon mutanen kirki. Shawarata anan ita ce; kowa ya nemi abokin tarayya na kirki.
Sunana Princess Fatimah Mazadu daga Gombe:
Lalacewar sun taru da rashin kame kai. Samarin kuma duk lalacewar mace sai da namiji.Ta hanyar daidaita sutura, wayo suturta jiki baki daya gudun shaidan, da sahaidanun duniya da shashashun maza. Dan duk sanda kika kasance mai killace jikinki ba wani sakarai ko shaidani da zai so ya kara kallonki sau biyu. Shawara shi ne Al’adar da suka bari su dawo da ita dan ba ta da amfani barinta; Sutura ta addinin musulunci, Rage yawan kule-kulen samari, rage yawan yawo, Rage yawan hira da kowani irin namiji, dan iska da shashashun maza, Yawaita zaman gida da tsare mutunci.
Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:
Abubuwan da ke janyo hakan yana da yawa, kadan daga cikinsu shi ne;, Rashin yin aure da wuri har sai mace ta kai shekaru fiye da ashirin, sannan wasu matan kwadayi na jawo masu fadawa hanyoyin da ba su dace ba, yin munanan kawaye nasa budurwa ta zama kamar bazawara. Laifinsu ne duka, amma na ‘yan matan ya fi yawa don su ke bada gudunmawar hakan 60% ko fiye da haka ma.
Hanyoyin magance matsalar sun hada da; yi wa ‘yan matan aure akan lokaci, biya musu bukatunsu na yau da kullum daga iyayensu, saka ido akan kawaye da samarin da suke tarayya da su, nuna musu illolin lalacewarsu tun kafin su kai minzalin balaga. Jin tsoron Allah, kokarin kamewa daga hanyoyin barna, nunawa iyaye bukatar aure da zarar an fahimci hakan shi ne bukata don gudun fadawa wata hanya ta daban.
Sunana Hauwa Jibrin Hotoro ‘Yan Katako Jihar Kano:
A tunanina abin da yake janyo wa maza su rinka yi wa ‘Yan mata kallon lalatattu sabida suma lalatattun ne, domin shi wanda zuciyarsa ba ta da kyau yana iya saurin zargin mace, sabida shi ma haka yake. Wasu matan kuma wayayyu ne, wayewar tasu ce zai sa wasu mazan su ringa yi musu kallon lalatattu. Gaskiya laifin ba za a danganta shi ace laifin maza ne ko mata ba, sai a hada duka 2. Dalili shi ne; yawanci game da harkar neman mata ita mace laifinta ya fi yawa, domin idan mace ba ta bada dama ba karya ne namiji ya nemeta sai dai rape, amma ko addini da Allah ya fara yana farawa da namiji ne, amma a bangaren zina sai ya fara da mace. Duk yadda mutun ya kai da lalacewa indan mace ba ta bashi dama ba sai ya hakura, su kuma maza suna da wani abu shi namiji ya fi mace hankali yana iya amfani da dukiyarsa da dabararsa da wayonsa ya nuna mata yana tare da ita ko da yaushe dan yanada wata bukata a ransa, sannan kuma zai iya amfani da rauninta duk dan ya sami abin da yake so daga gareta. Magancewa wannan abu ba wani abu ne me wahala ba, dadili shi ne; hanya 1 za a dauka shi ne kowa ta koma kan gwadabe na addinin kur’ani ya zo da magana, dai-dai da ado. Allah ya fadamaka iya mutanen da za ka bayyanawa adonka wato muharramanka komai ya fada maka, to idan aka koma wannan ina ga shi ne zai fi. Shawarar da zan bawa samari da ‘yan mata ita ce kowa ya ji tsoron Allah mu kyauta tawa junanmu zato, sannan kuma mata su tuna cewa duk sanda saurayi ya zo wajenki yana kaunarki indai bai miki ba ba ki ji kina san shi ba, kar ki karbi abin hannunsa, sannan shi ma namiji yarinya idan ba ta yi masa ba, baya jin kaunarta baya ganin zai iya aurarta kar ya je ya bata mata lokaci.
Sunana Abubakar Shehu daga Jihar Kano:
Yi wa ‘yan mata kallon Zawarawa (lalatatu) baban dalilin da ya sa samarin suke wa ‘yan mata kallon zawarawa (lalatatu), mafi yawancin ‘yan mata kaso 90% cikin dari ba sa kama kansu, kuma sannan wasunsu ba su san mutuncin kansu ba, suna abubuwan da ba su dace ba a ‘social media’ da suaransu. Wanda wanan shi yake bawa wasu bata garin samarin dama lalata wasu ‘yan matan. A nan dai kowa yana da nashi lafin su ‘yan mata nasu lafin su suke bawa samarin kofa ba sa kare mutuncinsu, su kuma samarin nasu laifinsu ba sa sa Allah a ransu su hakura har sai lokacinsu yayi. Daga cikin hanyoyin da za a magance malamanmu na adini su ci gaba da fadakar wa ana fadar ilolin matsalar, sanan gwamnati ta rinka daukar mummunan mataki akan irin wannan matsalar. Ni shawarata a nan ita ce mutunci ya fi komai, kuma su gyara matsalarsu da ubangijinsu.
Sunana Safiya Mustapha Mu’azu daga Gurin Gawa:
A zamanin yanzu wasu yan Matan suke zubarwa da wasu Matan mutumcinsu, yawanci ‘yan Matan yanzu suna da kwadayi abu kalilan za a basu a lalata musu Rayuwarsu, wacce iyayansu suka dade suna daurasu akai shekara da shekaru. Abin da ya sa ayanzu ‘yan mata suna yi shigar da ba ta dace ba, sa kananun kaya wanda baikamata musulma mai mutumci ace ta sa su ba hakan na janyo samari su mata kallon karuwa, wacce ta saba mu’amala da maza. A gaskiya laifin ‘yan mata ne domin sune suke yin abin da bai dace ba a yau, idan suka gyara dabi’unsu to samarin ma za su gyara kuma za su daina yi musu wannan kallon.
Hanyar magance wannan matsalar shi ne dola ne ‘yan mata su rage kwadayi da son abin duniya sa’annan iyaye su saka ido akan tarbiyyar yayansu, yanayin shigarsu da kuma samarin da suke mu’amala da su da kuma bincikar irin kudin da ‘ya’yansu ke kashewa idan har ba su suka basu ba sai su buncika, ‘ya’yansu inda suka samu, haka ne zai sa a magance wannan matsalar.
Shawarata ita ce ‘yan mata a rage kwadayi duk abin da iyayanki ba su yi miki ba ki sani babu wani da namiji da zai miki kuma ka da ki zama me hangen abin da kawayanki suke yi, domin kowa da irin tasa jarabawar idan kika yi hakuri wataran sai ki ga kin fi wannan kawar taki ki kame kanki a duk halin da kika tsinci kanki, sa’annan ki zama mai kai kukanki ga Allah in sha Allahu komai zai zo miki da sauki ba tare da kin sabawa ubangiji ba.
Sunana Abdullahi Dahiru Matazu (El-Suhab), Jiihar Katsina:
Babban dalilin da ya sa samari suke yi wa ‘yan mata kallon zawarawa shi ne; Duk abun da yarinya take bukata sai ka ji ta ce wa saurayinta ya yi mata. To matukar za ta bukaci wani abu wajensa, shi me zai hana shi bukata a wajenta. Laifin duka biyu ne, Idan ka san ba za ka taimake ta don Allah ba, to bai kamata ka ci dunduniyar ta ba. Idan kin san shi saurayi malalaci ne mai zai sa ki je wajensa. Ta hanyoyi guda biyu za a magance matsalar, Mu nemi yafiyar mahaifan mu, Sannan mu roke su su ci gaba da roka mana rahamar ubangiji. Idan ka/ki kuna cikin wannan sabgar to ba abun gori bane ya kamata ku gane cewa in an girma a san an girma. Idan akwai ilimi ayi amfani da shi, idan babu a tafi makaranta a nemo.
Sunana Musbahu Muhammad Goron Dutse Jihar Kano:
Samari Kan yi wa wasu Matan kallon lalatattu ne saboda yadda suke saka kaya da yadda suke gudanar da rayuwa maras kamun kai. Laifin dukkansu ne, su wasu matan sun ki su kame kansu, su kuma mazan tsabar sa’ido ne. Mata da mazan kowa ya koma kan koyarwar addinin Musulunci a harkokin rayuwarsu. Ya kamata Mace ta sani nutsuwarta da kamun kanta shi ne; Mutuncinta, kuma ta sani dukkan jikinta al’aura ne ban da fuskanta da tafiknta. Su kuma mazan su sani duk abin da kayi za ka maimaita shi a gaban Allah Idan ka yi wa Mace kazafi akwai ranar hisabi, dan haka a kame baki a fadi alheri ko ayi shiru.
Sunana Fatima Jaafar Abbas, Rimin Gado LGA Jihar Kano:
Gaskiya abin da yake janyo hakan shi ne; Kaucewar dokar musulunci da samari da ‘yan mata suka yi a wannan zamanin, Allah yana cewa: ka da ku kusanci Zina, amma mafi yawan samari da ‘Yan mata su kan kusantarta har ma wasu su dinga aikatawa, don haka sai mutane har ma da samarin su dinga ganin ‘yan matan a matsayin Lalatattu. Laifin dukkaninsu ne samari da kuma ‘yan matan. Hanyar da za a magance ita ce; iyaye su kara kula da tarbiyyar ‘ya’yansu ciki har da kula da kayansu su daina yawan “TABARRUJ ” ma’ana shigar da ba ta dace ba. Shawarata anan ita ce; samarin da ‘yan matan su kara jin tsoron Allah wajen kiyaye dokokinsa da kuma tsare mutuncin juna.
Sunana S.D Adam Unguwar Nungu Lafiya, Jihar Nassarawa:
Saboda ba su da kamun kai kuma jikinsu baya zama guri daya. Duk biyun suna da laifi, Addu’a ita ce mafita. Hanyar da za a magance; tarbiyya mai kyau tun yara suna tasowa, musanman ilimin Addini, Biya wa yara musanman mata bukatunsu. Su rinka kama kansu da kuma dagewa da Addu’a.