Assalamu alaikum. Malam akwai yaranmu da suke sana’ar siyar da koken da kayan maye, shin za su iya fitar da zakkar kudin da suka tara, idan sun kai nisabi?
Wa alaikumus salam. Dukkan abubuwan da suke sanya maye haramun ne siyensu da siyar da su da amfani da su, kamar yadda tarin hadisai da Kuma Aya ta (90) a suratul Ma’ida ta tabbatar.
Ba a fitarwa da dukiyar Haram zakka, saboda Allah Mai Tsarki ne ba ya amsar abu sai Mai Tsarki, kamar yadda Muslim ya rawaito.
Yana daga cikin manufofin zakka tsarkake dukiya kamar yadda Allah Ya fada a suratu Attauba, dukiyar da aka tara ta ta hanyar haramun najasa ce gaba dayanta, wannan yasa ba za ta tsarkaka ba.
Wanda ya wawuri kudin talakawa da bironsa, ba zai fitar musu da zakka ba, saboda ba mallakinsa ba ne.
Wanda ya gina masallaci da kudin haram, Allah ba zai gina masa gida a Aljanna ba, saboda najastaccen kudi ba ya isa zuwa ga Allah.
Wanda ya yi sadaka ko Ya gina gidan marayu da kudin Haram, Allah Ba zai ba shi lada ba.
Don neman karin bayani duba Almausu:a alfikhiyya 23/248.
Allah Ne Mafi Sani.