Miliyoyin mutane a ciki da wajen nahiyar Afirka sun kalli wasu bidiyoyi da ke nuna yadda wasu duwatsu ke samar da lantarki.
Daya daga cikin bidiyoyin ya nuna yadda wutar ke tartsasti yayin da aka hada duwatsun biyu, inda aka rubuta kalaman da ke cewa ”An samu duwatsun lantarki a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo”.
Wannan bidiyo ya yadu kamar wutar daji a lokacin da hamshakin kan kasuwar Afirkan nan Daniel Marben ya wallafa shi a shafinsa mai mabiya dubu 800 tare da rubuta Kalaman: ”Karin matsaloli na tunkaro mu, ina tausaya wa nahiyata Afirka”
Wani mai amfani da shafin Tuwita, ya yi tsokaci a kan bidiyon da Marben ya wallafa, ta hanyar wallafa wani bidiyo da ke nuna wani mutum rike da kwan lantarki kaure da wayoyi guda biyu inda kwan lantarkin ke kawo hasken wuta da zarar ya jona wayoyin a jikin wani karamin dutse da ke hannunsa.
Sa’o’i bayan nan ne kuma Marben ya sake wallafa wannan bidiyo a shafin nasa, inda fiye da mutum miliyan kaya suka kalle shi.
Fitaccen shafin Tuwitan nan mai suna ‘Africa Archibes’ ya sake wallafa duka bidiyoyin biyu, inda kaya daga cikin bidiyoyin aka kalle shi sau kusan miliyan 35.
To sai dai babu tabbas game gaskiyar lamarin duwatsun.
Bincike ya nuna cewa bidiyon farko da Marben ya wallafa, an fara wallafa shi a shafin Facebook na Jami’ar Mohamed na kaya, da ke Oujda a Morocco.
Inda aka rubuta kalmar ”Lithium!!?” ba tare da karin bayani ba.
BBC ta tuntubi Jami’ar, to sai dai har yanzu babu martani daga gare ta.
To amma abu mafi muhimmanci shi ne shin da gaske ne duwatsun da aka nuna a bidiyon za su iya rike ko samar da lantarki?
Dakta Ikenna Okonkwa malami a sashen koyar da ilimin ma’adinai na jami’ar Nijeriya ya ce ”ba zai yiwu ba”.
Ya ce “Duwatsun sun yi kama da ma’adinin zinc ko dalma, don haka ba su da karfin ma’adinin da zai samar da lantarki”.
Za su iya rike wutar da ire-iren ma’adinai irinsa ke da ita, to amma ba ta da karfin da za ta haska kwan lantarki”, in ji Dakta Okonkwo.
Don haka a ganinsa wannan bidiyo kawai wani ”siddabaru ne”.