Sakamakon ruwan saman da ake maka wa kamar da bakin kwarya, ya janyo ambaliyar ruwa, da zaftarewar kasa, tare da asarar rayukan mutum 59 a Kasar Indiya da Bangladesh.
BBC ta rahoto cewa Masu aikin ceto, sun bazama neman mutanen da suka bace a yankunan kasashen da lamarin ya shafa, domin kai su tudun mun tsira.
Yawancin wadanda suka mutu a Bangladesh, tsawa ce ta fada musu.
An dakatar da tashi da saukar jiragen sama, yayin da aka soke jiragen kasa da manyan motocin bas da ke sufuri a manyan tituna.