Kasashen Amurka da Japan sun hana kasuwancin fitar da sassan na’urorin laturoni zuwa kasar Sin. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana a yau Jumma’a cewa, ya kamata Amurka ta dakatar da daukar matakan sanya takunkumi bisa radin kanta, kuma ba bisa doka ba. Kana, ta daina yin shisshigi cikin harkokin sauran kasashe, ta kuma sauke nauyin dake wuyanta, a matsayin ta na zaunanniyar memba a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Rahotanni sun ce, bisa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Amurka da Japan da Holland kwanan nan, za’a fadada haramcin da Amurka ta yi, na fitar da sassan na’urorin laturoni zuwa kasar Sin, zuwa kamfanonin kasashen Japan da Holland. Manazarta sun ce, Amurka ta haramta wa sauran wasu kasashe fitar da kayayyakin su zuwa kasar Sin, bisa shirin dokar dake aiki a kasar kadai, wanda ya zama tsoma baki cikin harkokin sauran kasashe. (Murtala Zhang)