Mataimakin ministan ma’aikatar kare muhalli, ayyukan gona da kiwo a kasar Burundi Emmanuel Ndorimana, ya godewa tawaga ta 5, ta kwararrun masana aikin gona ta kasar Sin, wadda ta kammala ayyukan tallafawa kasar a fannin raya noma.
Mr. Ndorimana, wanda ya bayyana hakan da yammacin ranar Juma’a, yayin bikin ban kwana da tawagar da aka gudanar a ofishin jakadancin Sin dake Burundi, ya ce kasar sa ta yi matukar gamsuwa, da nasarorin da aka cimma, karkashin tallafin tawagar masanan ta Sin.
Ya ce, karkashin manufofin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka na FOCAC, tawagogin masana aikin gona 5 na kasar Sin, sun gudanar da ayyuka a Burundi, domin taimakawa kasar dake gabashin Afirka da dabarun bunkasa noma.
Bisa jimilla, kwararrun masanan na Sin 45, cikin tawagogi 5 ne suka gudanar da ayyuka a kasar, kuma kwazon su, da jajircewa wajen gwajin sabbin iri da fasahohi, da yadda suka rika horas da karin ma’aikata a fannin, da bunkasa masana’antu masu nasaba, da tsara matakan aiwatar da manyan ayyuka, sun samu yabo matuka daga al’ummu, da manoma, da sauran abokan huldar su dake Burundi.
A bangaren noman shinkafa, Ndorimana ya ce, tawagar kwararrun ta cimma nasarar zabar irin da aka tagwaita mafi dacewa da Burundi, wanda ke iya samar da yabanya da yawan ta ya kai kusan tan 12 a duk hekta. (Saminu Alhassan)