A ranar Lahadi al’umar Garin Tudun Wada da ke Ƙaramar Hukumar Tudun Wada ta Jihar Kano Suka gamu da ibtila’in rikicin siyasa da ya barke tsakanin magoya bayan Jam’iyyun NNPP Da APC wanda hakan ya haifar da kone-konen motoci da dukiyoyin al’uma.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta tseguntawa Wakilinmu cewa an kashe mutum guda cikin magoya bayan Jam’iyyar NNPP.
- Ganduje Ya Amince Da Fara Daukar Fasinjoji Kyauta Ba Kudi A Motocin Gwamnatin Kano
- APC Ta Dage Yakin Zaben Shugaban Kasarta A Kano
Arangamar ta samo asali tun ranar litinin lokacin da Jam’iyyar NNPP ta tsara gudanar da taronta, inda wata majiyar ma ta ce an hana su gudanar da tarontun da farko,
Ko a ranakun Juma’a da Asabar duk Sai da aka fara hangen yadda wasu gungun matasa dauke da makamai sun fito inda Jami’an tsaron sojoji da ‘Yansanda suka tarwatsa su.
Kwatsam sai dai a ranar Lahadi rikicin ya sake barkewa inda aka Fara kone-kone tare farmakar juna tsakanin ‘yan Jam’iyyun biyu na NNPP da APC.
Rahotonnin da muka samu sun shaida mana cewa a rangamar ta yi sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da Kona Motoci tara duk da ba’a asamu sanarwar mutuwar mutum ko daya ba a hukumance.
Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai Kuma. bata fayyace batun mutuwar mutum guda din ba, Haka kuma rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar kwantar da tarzomar yayin da Jama’a suka koma bakin harkokinsu na yau da kullum kamar yadda aka saba.
Ita dai wannan Karamar Hukuma tare da takwararta Karamar Hukumar Doguwa na fuskantar irin wadannan tashe-tashen hankula ne sakamakon yadda ‘yan siyasa musamman ‘yan takarkarun Jam’iyyun NNPP da APC a lokuta daban-daban ke yawaita nunawa juna yatsa a tsakaninsu.