Wani matashi mai suna Musa Lurwanu Maje, ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, bayan da dubunsa ta cika bisa zargin damfarar mutane a Facebook da sunan mace.
Maje, wanda ke amfani da sunan wata matashiya mai suna Zahra Mansur a shafin na sada zumuntar, ya shiga hannun ‘yan sanda ne bayan jama’a da dama suka dinga korafe-korafe a kansa a Facebook.
- Kungiyar Jaruman Nollywood Ta Dakatar Da Moses Armstrong Kan Zargin Yi Wa Yarinya Fyade
- Wasu Gungun Barayi Sun Afka Ofishin Premium Times Sun Kone Ofis Da Kayan Aiki Kurmus A Kano
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranarLahadi.
Maje ya shiga hannu ne bayan da Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya bada umarnin cafko shi.
Kiyawa ya ce tuni matashin mai shekara 26 ya shiga hannun rundunar inda yanzu haka ake gudanar da bincike a kansa.
Kiyawa, ya kuma bayyana cewa an samu wayar hannu kirar Redmi Note 11 Pro, wadda darajarta ta kai N200,000 da kudi N70,000 da sauran abubuwa da ya samu wajen damfarar al’umma.
Kazalika, an samu hotuna da bidiyon batsa na mutane da dama wanda da su matashin ya ke amfani wajen samun kudi a hannun wadanda ya ke damfara.
Kiyawa ya ce za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike a kansa.