Babbar Kotun Jihar Jigawa da ke Birnin Kudu ta yanke wa Isyaku Wakili Gwanto hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe Malama Malora Adamu.
Tun da farko dai an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bisa zargin fille kan matar da adda a matsugunin Fulani Duliyari da ke karamar hukumar Kirikasamma.
- NECO Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar Watan Nuwamban 2022
- DSS Ta Gargadi ‘Yan Siyasa Da Yada Labaran Karya
Alkalin kotun, Mai shari’a Musa Ubale ya ce laifin kisan kai ne da hukuncin kisa a karkashin sashe na 221 (b) na kundin laifuffuka.
Mai shari’a Ubale ya ce lauyan mai shigar da kara ya tabbatar da kararsa ba tare da wata shakka ba, don haka ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya domin ya zama izina ga wasu.