An gudanar da taron zaunannen kwamitin membobin ofishin siyasa, na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin a yau, inda aka saurari bayani game da yanayin yaki da cutar COVID-19 na kasar Sin a wannan lokaci.
A gun taron, an yi nuni da cewa, a cikin shekaru fiye da 3 da suka wuce, kwamitin tsakiya na JKS, ya tsaya tsayin daka kan manufar maida jama’a da rayuwarsu a gaban komai, an kuma yi hadin gwiwa a tsakanin jama’a daga kabilu daban daban na dukkan kasar Sin, don yaki da cutar COVID-19 bisa jagorancin JKS, da daidaita matakan yaki da cutar bisa yanayin da ake ciki, da daidaita matsalar dake shafar bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar, yayin da ake yaki da cutar, da magance yaduwar nau’in cutar mafi kawo illa ga lafiyar jama’a a kasar, inda ta hakan aka tabbatar da rayuka da lafiyar jama’ar kasar.
Tun daga watan Nuwanbar bara, bisa manufar kiyaye lafiya da magance samun wadanda suka kamu da cutar mafi tsanani, Sin ta kyautata matakan yaki da cutar, da sassauta yanayin tinkarar yaduwar ta cikin sauri, da samun babbar nasara a yaki da cutar.
An jaddada cewa, a halin yanzu, Sin tana fuskantar kyautatuwar yanayin tinkarar cutar, amma ana ci gaba da samun yaduwar ta a duniya, kana an kiyaye samun canjin nau’in cutar. Don haka ya kamata hukumomi na wurare daban daban dake kasar Sin, su kyautata tsari, da matakai game da wannan batu, da aiwatar da ayyukan yaki da cutar a sabon mataki, da inganta tsarin kiwon lafiya, don tabbatar da yanayi mai kyau da Sin take ciki a yanzu. (Zainab)