Kungiyar Matasan Arewa Mazauna Legas, ta jaddada kira ga al’ummar arewa da cewa bai kamata yankin ya yi sakaci har ya koma gidan jiya ba dangane da halin ha’ula’in da aka jefa shi ciki na tashe-tashen hankula da kangin talauci da karayar tattalin arziki.
Kungiyar ta sake nanata kiran ne sakamakon abin da ta kira “yunkurin wasu marasa kishin al’ummar yankin na sake mayar da shi gidan jiya domin biyan muradun kashin kansu a zaben 2023 da ke tafe”.
- Arewa An Sha Mu Mun Warke, Bai Kamata Mu Koma Gidan Jiya Ba – Matasan Arewa A Kudu
- Hukumar Harkokin Waje Ta NPC Ta Fitar Da Sanarwa Kan Kudurin Amurka Game Da Shigar Balan Balan Din Sin Samaniyar Amurka
Kungiyar wadda ta yi kiran ta bakin shugabanta, Alhaji Ibrahim Yaro Galadanci, ta kara da cewa dangane da zaben 2023 musammam na shugaban kasa mun ji yadda wasu shugabanni daga arewa suke babatu domin cikar burinsu na son zuciya, suna so a goyi bayan wadanda za su kara kashe mana yanki, marasa rikon amana, to muna fada wa mutanen arewa cewa wannan baa bin amicewa ba ne a gare su, sannan su kuma masu yi su san cewa komai nisan jifa kasa zai sauko.”
Kungiyar ta ci gaba da cewa tun daga dawowar mulkin dimokuradiyya ake wa yankin zagon kasa kuma idan har ba a farga a wannan lokaci na zabe ba, za a yi aikin da-na-sani.
“Domin lokaci ya yi da za mu zama tsintsiya madaurinmu daya, wallahi tsakanin musulmin arewa da kiristocin arewa kowa ya sani tun a shekarar 1999 aka shirya kawar da dukkan ‘yan arewa daga doran kasa, aka dinga yi mana kisan gilla, ana kona dukiyarmu amma sabo da baragurbin shugabanni da suka mayar da mu saniyar ware, babu wasu masu kwatar wa ‘yan arewa ‘yanci. Duk inda ake rigima dan arewa ake kashewa, waye bai da masaniyar hakan a wannan lokacin.
“Dan haka muna kira da babbar murya, babu yaudara wallahi, lallai mu kwatar wa kanmu ‘yanci domin mafitarmu a yanzu shi ne hadin kai mai karfin gaske wanda dole mu samu sauyi da taimakon Allah, mu yi kokarin hada kan kwankwaso da Al-Musatapa domin arewa muna da makama. Duk arzikin da Allah ya shinfida a karkashin kasa yana yankin arewa, tun daga kan Gold (Zinare) da manyan ma’adanai wadanda ka da mu yi sake masu cewa su ne shugabaninmu su sayar da mu tun da sun kasance karnukan farautar wadansu.” In ji shugaban kungiyar.
Har ila yau, kungiyar ta yi waiwaye adon tafiya game da manyan rikice-rikicen da ta ce an kirkiro domin wargaza yankin, “masu hada wadannan rigingimu da makirce-makice sun cire rahamar Allah a zukatansu, suka bari aka kirkiro Boko Haram, aka kirkiro rigimar manoma da makiyaya, saboda dukiyar da take Maiduguri da Yobe da Zamfara da Sakkoto da Neja da Kogi duk duniya babu kasar da za ta iya ja da arzikin da Allah ya yi mana, amma kuma ga mutanenmu suna cikin yunwa da talauci, don haka mu zabi ‘yan siyasa masu kishin al’umma da za su iya kawo gyara.”
Alhaji Ibrahim ya kuma nunar da cewa ba saboda wata jam’iyya daya suke wadannan kiraye-kirayen ba, yana mai cewa, “dan ba ma jam’iyya, abin da muke so mutanenmu na arewa su yi kawai, mu yi kokarin janyo hankulan `yan’uwanmu wadanda suna cikin duhu da su dawo hanya domin mu ceci rayuwarmu, muna da arziki, don haka a daina yi mana kisan gillah. Sannan a yi kokarin daidaita tafiyar Majo Hamza Al-Musatapa da Kwankwaso, wallahi alheri ne a gare mu, dan Allah mu yi wa azzaliman tsofaffin shugabaninmu bara’a lokaci domin wannan ne lokaci mafi dacewa da za mu nema wa kanmu mafita.”
Wakazalika, kungiyar ta matasan arewa ta ce taron da gwamnonin Nijeriya suka yi da shugaban kasa a kan batun canjin kudi ba don talakawa suka yi ba, “taron da suka je Abuja suka samu shugaban kasa a fadarsa sabo da maganar canjing kudi domin kansu ne ba don talaka ba. Don su ma za su yi asara shi ya sa suka je, saboda mutum nawa aka sace a arewa ban da wadanda aka yi wa kisan gilla, me ya sa babu wanda ya ce ya kamata su yi kungiya dan hakan? Lallai ya zama wajibi mutane mu farka mu yi wa kanmu kiyamullaili.” In ji Galadanci.