Jamiyyar PDP cikin wata sanarwa da kakakinta na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar, ta yi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya tilasta wa ‘Yan APC da gwamonin jam’iyyar da kuma dan takarar shugaban kasa na APC, da su saki biliyoyin sabbin takardun kudin da suka boye don sayen kuri’a a zabukan 2023.
Ta yi wannan kiran ne biyo bayan karancin sabbin takardun kudaden da ake ci gaba da fuskanta a daukacin fadin kasar nan.
- Da Dumi-Dumi: Jam’iyyar PDP Ta Soke Gangamin Yakin Neman Zabenta A Jihar Ribas
- Wani Ya Rasu Yayin Da Magoya Bayan APC Da PDP Suka Yi Arangama Da Juna A Jigawa
Ologunagba, ya ci gaba da cewa, a jawabin da Buhari ya yi wa ‘yan Nijeriya ranar Alhamis ya sanar da cewa, tsarin na sauya kudaden tsarin gwamnatin APC ne wacce ke sa ido kan yadda ake sarrafa sabbin kudaden da zagayawar su a cikin aluma.
Ya kara da cewa, hakan ya nuna a zahiri babu hannun jamiyyar PDP a cikin wannan tsarin, inda ya sanar da cewa, tun a baya PDP ta ankarar da ‘Yan Nijeriya kan zagon kasa da ake yi na karkata sabbin takardun kudaden don cimma burin shirin su na cin zabe a 2023.
Ya ce, PDP na tausaya wa ‘yan Nijeriya kan wannan karancin sabbin takardun kudaden da suke ci gaba da fuskanta, inda ya kara da cewa, PDP ta tona asirin gwamnonin APC bisa zarginsu da boye sabbin kudaden a wata maboyar da ke a jihohin Legas, Kano, Kogi, Kaduna, Imo da sauransu don kawai su sayi kuri’un masu kada kuri’a a kasar nan.
Ologunagba ya yi ikirarin cewa, ko a kwanan baya PDP ta ankarar kan yadda kwamitin yakin neman zaben Tinubu da Shettima suka kitsa karancin sabbin takardun kudaden ganin cewa, ‘yan Nijeriya ba sa goyon bayan takararsu.