Tawagar Jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa NIS mai Mutum Takwas ta kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu hedikwatar Hukumar Kula da Kan iyakokin Turai FRONTEX a makon da ya gabata don tattaunawa da Jami’an hukumar kan harkokin tsaro da kula da bakin haure.
Tawagar wacce mataimakin Kwanturola Janar, Muhammad Aminu Muhammad mni, mai kula da sashes tsaron iyakokin Nijeriya ya jagoranta, ta samu tarba daga manyan jami’an hukumar FRONTEX karkashin jagorancin Mista Iain Galea a hedkwatar FRONTEX da ke Warsaw a kasar Poland.
A jawabinta na maraba, shugabar riko ta FRONTEX Aija Kalnaja ta bayyana cewa hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya (NIS) aminiyar hukumarsu ce ta FRONTEX a fannin tsaro da kula da bakin haure.
Kalnaja ta jaddada cewa dangantakar da ke tsakanin hukumar FRONTEX da NIS ta samo asali ce tun a shekarar 2012 lokacin da hukumomin biyu suka shiga cikin wani tsari na aiki kan tsaro kan iyaka da kula da bakin haure.
Ta kuma sake gabatar da bukatar sake inganta hadin gwiwa daga hukumomin kan iyakoki don ci gaba da yaki da laifuffukan fasa kwari musamman masu safarar Mutane da haramtattun kaya.
“Ina fatan dukkan hukumomin biyu za su yi amfani da cin moriyar wannan taron don sake nazarin tsarin Ayyuka don ganin ko akwai wuraren da za a iya sake ingantawa su yi daidai da tsarin zamani” in ji ta.
A jawabin godiyarsa, shugaban tawagar NIS kuma shugaban sashen kula da kan iyakoki, DCG Aminu Muhammad ya bayyana jin dadinsa da irin tarbar da aka yi wa tawagarsa, inda Ya sake nanata kwakkwaran kudurin NIS na samar da ingantacciyar hadin gwiwa da hukumomin tsaro na kan iyakoki, kamar irin su FRONTEX sannan kuma ya yi kira ga bangarori biyun su tattauna manyan kalubalen bangarorin a yayin gudanar da taron.
DCG Muhammad ya kuma jaddada bukatar da ke akwai ta ganin kasashen Turai da sauran kasashen da suka ci gaba sun yi bitar shirye-shirye masu dorewa na hadin kai da hukumomi domin shawo kan matsalolin abubuwan da suke jawo yin kaura a wannan zamani fiye da kafa shinge kan iyakoki don shawo kan kwararowar bakin haure.
Ya nusar da cewa kudaden da ake kashewa na gina manyan shinge kan iyakoki ba zai samar da fa’ida mai dorewa ba idan yanayin rayuwar jama’a a kasashe masu tasowa ya kasance cikin mawuyacin hali.
Tun da farko, wanda ya shirya tafiyar zuwa hukumar FRONTEX, wakilin kasar a FIIAPP, shiri mai kula da yaki da fataucin mutane da safarar bakin haure a Nijeriya (A-TIPSOM), Mista Rafael Molina ya bayyana cewa ofishinsa ya yanke shawarar tsara tafiyar ce da nufin habaka hadin gwiwa tsakanin FRONTEX da NIS don yaki da balaguro mara ka’ida kuma mai hadari.
An dauki lokaci mai tsawo ana tattauna muhimman al’amura kamar tsarin Hijira da aiki da na’urar tantance bayanan matafiya ta (MIDAS), da kuma tsarin Cibiyar Nazarin Hijira ta NIS da sauransu.
Wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka fi daukar hankali a taron sun hada da nuna kwarin gwiwa wajen inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin biyu wajen yaki da hijira ba bisa ka’ida ba tare da bayar da tabbaci mai karfi na inganta ayyukan samar da bayanai a tsakanin hukumomin biyu.
Bayan kammala Taron, tawagar jami’an NIS sun ziyarci ofishin jakadancin Nijeriya inda suka samu tarba ta musammam daga Ambasada Manjo Janar mai ritaya, Christian C Ugwu, wakilin Nijeriya a kasar Poland da abokan aikinsa.
Tuni dai tawagar hukumar ta NIS ta dawo gida lami da lafiya, inda ta sauka a Abuja Nijeriya.