Dantakarar sanata a karkashin inuwar jam’iyyar PRP a shiyya ta daya Abdullahi Ahmada Waili, ya bukaci al’umma musamman na mazabarsa da su tabbata sun fito, gobe asabar domin yin zabe, kuma su tabbatar sun zabi wanda zai kasance yare da su a kowane lokaci, wanda ya san bukatunsu nay au da kullum.
Wakili ya ce, yanzu loacin siyasar kudi ya wuce, lokaci ne da ya kamata al’umma su kara nutsuwa wajen zaben wanda ya cancanta ya shugabance su.
- Kotu Ta Sake Aike Murja Da Wasu ‘Yan TikTok 3 Zuwa Gidan Yari
- Da Dumi-Dumi: Sergio Ramos Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Sifaniya Kwallo
Saboda haka sai ya jaddada kiransa, wanda ya ce, muna kara kira ga musamman ga matasa da su duba halin da ake ciki a yanzu, su yi anfani da kuri’ansu, su zabi shuwagabanni na gari, wadanda za su ji tausayinmu su dubi halin da ake ciki a wannan kasa.
Al’ umma su sani ba a samun shuwagabanni sai ta hanyar zabe, don haka kada a ki fito wa a yi zabe. A fito, a duba cancanta.
Mu ku la da sayar da hakkinmu ta hanyar karbar kudi.
Saboda, ta haka ne gurba tattun mutane ke samun hanyar dari wa mulki su yi ta gallaza wa jama’a. Amma idan muka ki amsar kudi muka zabi shuwagabannin da suka cancanta sai a samu shgabanni na gari.
Saboda haka muke kira da babbar murya musaman ga matasa da su guje wa bangar siyasa, ka da su bari a yi amfani da su wurin tayar da hankalin al’ umma.