Yayin da aski yazo gaban goshi al’amarin ranar babban zabe sai kara karatowa take duk wasu shirye- shiryen kuma an aiwatar da su an kammala,wannan yasa ita hukumar zabe mai zaman kanta ta bada sanarwar ranakun da za a aiwatar da zabubbukan da za ayi a watannin Fabrairu da Maris na shekarar 2023.
Hukumar ta bayyana hakanne a shafinta na Twitter.
- Yadda Gwamnonin Nijeriya Suka Butulce Wa Shugaba Buhari Bayan Ya Fitar Da Su Kunya
- Da Dumi-Dumi: Sergio Ramos Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Sifaniya Kwallo
Kamar yadda hukuma ta tsara akwai sharudda bakwai da suka kamata a cika su kafin ayi zabe.
Zamu kalli su wadannan sharuddan zabubbuka a Nijeriya daya bayan daya
Nau’oin zabe nawa ne a Nijeriya?
Zabubbuka ana yin sune lokaci zuwa lokaci na mukaman ofisoshi daban- daban a Jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tsarin mulki ya bada damar kafata domin akan kuduri ko dokar tsarin mulkin kasa,da ya bada na kafa tane, domin ta aiwatar da zabubbuka a Nijeriya.Zabubbukan sun hada da na ofisoshin Shugaban kasa, mataimakinsa , mambobi na majalisun Jihohi, Gwamnoni da mataimakansu,‘yan majalisun Dattawa da kuma na Wakilai ta tarayya.
Duk da haka akwai wadansu matakai na ayyukan da ake yi lokacin da ake zabubbuka a Nijeriya.
Wadannan matakan zabubbuka a Nijeriya sun hada da kafin ayi shi zaben akwai zabubbukan fidda gwani,inda za ace ga wanda ko wadda ta dace, kamfen ko yakin neman zabe da dai sauransu.
Mataki kafin ayi zabe
Wannan matakin daya kunshi yadda za fito da su ‘yan takarar daga jam’iyyun siyasa, domin sune suke bayyana maufofinsu ga al’umma.A wannan matakin ne duk wadanda suka cancanci kada kuri’a suke yin rajista da hukumar zabe mai zaman kanta.Daganan kuma ne hukumar zata bada sanarwar ranar zabe inda ta haka ne aka fara bin matakan yin zaben.
Zaben fidda gwani: A wannan matakin ne su ‘yan takarar da suke bukatar a tsai dasu takarar mukamin ofishin da suke bukata,inda za a fara ne da tantancesu tukuna, domin samun damar cancanta ta tsayawa jam’iyyinsu don su samu damar fafatwa da sauran ‘yan takarar na wasu jam’iyyun a babban zabe.
Tsai da ‘yantakara: Anan ko wace jam’iyyar siyasa zata bada dantakara ko ‘yar takararta daya da zai ko zata tsayawa jam’iyyar.Duk dantakara ko ’yartakara da aka zaba na jam’iyya dole ne, ya ko ta cika duka sharudda kamar yadda dokar zabe ta bayyana, tsarin mulki na kasa da kuma ka’idojin hukumar zabe mai zaman kanta.
Kamfe: Wannan matakin ne da jam’iyyun siyasa da ‘yantakararsu ne zasu fara kamfen babu kama hannun yaro domin neman taimakon wadanda suka gamsu da manufofinsu har su yanke shawara ta zaben su,kamar yadda hukumar ta ware wani lokaci na yin hakan.
An amince masu da zuwa kamfe Jihohi daban- daban, kafofin yada labarai da kuma na sanardawa na zamani.Sauran matakan sun hada da cancance masu kada kuri’a:
Hukumar zabe anan ta bayyana yadda za a kada kuri’ar ta hanyar amfani da BBAS.
Kawo kuri’u da kayan zabe a rumfar yin zabe Wannan ya hada da ita hukumar zata samar ko kawo kuri’u da sauran abubuwan da suka kamata da za ayi amafani dasu wajen aiwatar da zabe kamar yadda doka ta shimfida.
Sauran abubuwan da za ayi sune kada kuri’a,tara kuri’un da aka kada, kirga su kuri’un da masu zabe suka kada a rumfar bayan an ware marasa kyau, da bayyana sakamako na yawn kuri’un da kowane dantakara ko ‘yar takara suka samu.
Kafin hukumar zabe mai zaman kanta ta bullo da na’urar (BBAS), hukumar tayi amfani ne da na’urorin Smartcard Reader da kuma Z-pad wajen aiwatar da zabubbuka.Sai dai kuma a wannan karon hukumar ta amince da yin amfani da na’urar BBAS da aka fara amfani da ita a shekarar 2021.Tuni aka yi amfani da na’urar BBAS a zabubbukan da aka yi a shekarun baya.
Kamar yadda hukumar ta bayyana dalilin amfani da na’urar BBAS ta yi hakan ne domin sake ba ‘yan Nijeriya kwarin gwiwa na tabbatar da za ayi sahihai kuma zabubbukan da za a amince da sakamakonsu a Nijeriya.
Bugu da kari ma hukumar ta kawo wasu fasahohi a baya da suka hada da katin zaben dindindin da ya kunshi wasu muhimman bayanai na mai katin, wanda shi ne ya maye katin zabe wanda ba na dindindin ba da aka yi amfani da shi a babban zabe na shekarar 2011.
Hakanan ma hukumar tayi amfani da na’urar tantance tambarin yatsun mai kada kuri’a wajen tantancewa karo na farko a zabubbukan shekarar 2015.
Na’urar card reader tana nuna hoton mutumin daya mallaki katin wanda hakan ne zai ba ma’aikatan zabe damar gane ko shi ne mai katin, hakanan ma yana bada dama ta tantance tambarin hannu.
Yana bada dama ta tantance tambarin yatsa na masu zabe da wadansu bayanan da suka dace a sani nasu a cikin katin na PBC.
Wadanne sharudda ne da sai an yi su kafin zabe?
A Nijeriya zabubbukan ana yin sune ranar Asabar kamar yadda dokokin hukumar zabe mai zaman kanta ta tanada.
Kamar yadda dokokin suka bayyana yakamata a fara zabe karfe takwas da rabi na safe lokacin ne za a fara tantance jama’ar da suka zo yin zabe, daga karfe takwas wanda lokacin ne za a bude su rumfunan zaben, domin tantance mutane a kuma rufe karfe daya na rana.Wannan yana nuna duk mutanen da suka je wurin kafin karfe daya na rana za a tantance su.
Ana sa ran wadanda suka cancanci yin zabe su je wurin da suka yi rajistar katin zabe,ko kuma rumfar da hukumar ta maida su don yin zabe.
Dole ne wanda ko wadda ya ko ta cancanci yin zabe su kasance ‘yan Nijeriya ne da suka kai shekara goma shatakwas, sun yi rajistar a wurin da suke son yin zaben,inda zasu je tare da katin zaben da suka yi rajistar.
Mataki na gaba kuma shine bada katin zabe na dindindin (PBC)don tantance mai katin ta amfani da na’urar (BBAS).Ita BBAS wata na’ura ce da aka yi domin ta tantance katin mai zabe domin gane sahihancin shi a ranar zabe.
Na’urar BBAS tana bada damar ganewa ta hanyar wata fasaha wajen gano hakikanin al’amarin ta hanyar tambarin dan yatsa da yadda fuskar take.
Na’urar tana iya daukar hoton rumfar zaben da shi hoton sakamakon zaben da aka rubuta a (Form EC8A)da hoton takardar da ake rubuta sakamako na hukumar zabe wanda za a tura a kuma gan shi ta kafar sadarwa ta zamani (IReB).
Ita IReB wata kaface ta sadarwa ta zamani inda sakamakon daga runfunan zabe za a wallafa su domin mutane su gani.
Kafar tana ba mutane dama ta samar dawata hanya domin damar samun sakamako daga wasu mazabu ta kafar sadarwa ta zamani.
Mataki na uku shine a bincika da tabbatar da cewa sunan mai katin zaben yana cikin rajistar masu zabe ta wannan rumfar.Matakin yana da sauki saboda kuwa su masu zaben suna iya ganin sunayensu a kafar sadarwar zamani ta INEC,da take nuna rumfunan da zasu yi zabe da duk wadansu bayanan da suka kamata.
Abinda zai biyo bayan wannan shine tabbatar da sahihancin amfani da na’urar BBAS wajen tambarin hannu da gane fuska.
Da zarar an tantance jami’in zabe mai kula da rumfar zai ba shi mutumin daya mallaki katin kuri’ar da zai zabi dan takarar da yake so ya zaba, bayan shi jami’in zaben ya bayyana ma su matakan da masu zaben zasu bi. Daganan sai shi jami’in zaben ya umarci duk wadanda aka tantance su yi layi daya domin abu ya tafi cikin sauki ba tare da yamutsi ba.
Daganan sai zuwa wurin da aka ajiye akwatunan zabe inda ake sa ran wanda zai kada kuri’a zai zabi wanda yake so cikin sirri, bayan yayi hakan sai ya sa kuri’ar a cikin akwatin zaben.Sai kuma ya je wurin mataimakin jami’in zabe na biyu.
Mataimakin jami’in zabe na biyu ne zai sa ma wadanda suka kada kuri’a Tauwada bayan sun kada kuria’rsu domin gudun kada wasu su sake dawowa su ce za su sake yin zabe.
Bayan kada kuri’a da sa ma wadanda suka kada kuri’a da sa masu Tauwada a dan yatsa, wanda suka kada kuri’ar, daganan suna iya tafiya gida ko su bar wurin zaben da akalla mita 300 domin su ga yadda za a ware kuri’u masu kyau da wadanda basu dakyau da kuma kirga su.
Jami’an zabe su ke da dama ta ware kuri’u da kuma kirgawa, da bayyana sakamakon zaben na rumfunan zaben kafin su ba wadanda ya dace su ba.
Su zabubbukan za ayi sune a watannin Fabrairu da Maris.Zaben Shugaban kasa da na ‘yam majalisun Dattawa da Wakilai na kasa ranar25 Fabrairu ranar Asabar 25 ga Fabrairu 2023, yayin dana Gwamnoni da ‘yan majalisun jiha za ayi shi ranar Asabar 11 ga Maris 11 2023.
Bada dadewa bane hukumar zaben ta bada sanarwa ta wadanda aka mai da su wasu rumfunan zabe, za’a sanar dasu ta hanyar sakonnin kar- ta- kwana wato.
Ta bayyana matakan da aka dauka na mai da wasu masu rumfunan zabe, an yi hakan ne domin a samu sauki lokacin kada kuri’aI,dalili kuwa wasu rumfunan zaben suna da mutane masu zabe da yawa, yayin da wasu kuma suke da mutane kadan.