Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gaza samun nasara a rumfar zabensa ta Yahaya Umaru mai lamba 010 da ke gundumar Jekadafari, inda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe akwatinsa.
Wakilinmu ya rawaito cewar shi ne Ko’odinetan yakin zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu amma ya kasa kawo masa rumfar zabensa.
- Da Dumi-Dumi: Obi Ya Lashe Mazabar Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa
- Mutum 5 Sun Jikkata Yayin Da Boko Haram Suka Kai Hari Wajen Zabe A Borno
Jami’in zabe a rumfar zaben gwamnan, Mishel Thomas, wanda ya sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar, ya ce, PDP ta lashe zaben da kuri’u 215, yayin da dan takarar APC, Bola Tinubu ya samu kuri’u 186 kacal.
Kazalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya samu kuri’u 10 kacal, inda shi kuma na LP, Peter Obi ya samu kuri’a hudu kacal.