Babban bankin kasar Iraki ya bullo da wasu sabbin matakan kyautata kudaden ajiyar kasar, ciki har da yarda da amfani da kudin kasar Sin wato RMB kai tsaye don gudanar da cinikayya tsakanin Iraki da Sin.
Yayin zantawar wani masanin tattalin arzikin kasar Iraki, Dr. Abdul Rahman Al-Mashhadani da wakilin CMG, game da wannan batu, ya bayyana cewa, ‘yan kasuwan Iraki na son ficewa daga tsaikon dalar Amurka, don haka, wannan kuduri na babban bankin kasar na da matukar muhimmanci.
Dr. Abdul Rahman Al-Mashhadani ya yi karin haske cewa, bisa hasashen da aka yi, kudin Sin wato RMB zai samu karbuwa sosai, saboda ‘yan kasuwan Iraki da yawa ba su son amfani da dalar Amurka.
Makasudin babban bankin Iraki na bullo da sabbin matakan shi ne, fadada hanyoyin jawo jari. ‘Yan kasuwan Iraki suna fuskantar babban matsin lamba wajen musanyar kudade, inda suke fatan kawar da cikas da asusun ajiyar Amurka ke haifarwa, matakin da zai taimaka ga kara fadada harkokin kasuwanci. (Murtala Zhang)