Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar a Kebbi da kuri’u 285,175.
Jami’in tattara sakamakon zaben na jihar, Farfesa Usman Sa’idu a lokacin da yake gabatar da sakamakon a Birnin Kebbi, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Bola Tinubu ya samu kuri’u 248,088.
- Tawagar Masu Aikin Jinya Ta Kasar Sin Dake Kasar Togo Ta Yi Aikin Jinya Kyauta
- Sin Za Ta Ci Gaba Da Taka Rawa Wajen Daidaita Matsalar Basussukan Zambiya
Saidu ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, shi ma ya samu kuri’u 10,682 yayin da jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya samu kuri’u 5,038.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan bayyana sakamakon, babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, Alhaji Bala Dole ya bayyana jin dadinsa da hakan.
Ya yi iƙirarin cewa idan ba don wasu “kananan kura-kurai” da jam’iyyarsa ta samu kuri’u masu yawan gaske.
Hakazalika, Wakilin jam’iyyar APC, Alhaji Ja’afar Ahmed, ya ce akwai batutuwan da suka shafi sakamakon, inda ya jaddada cewa, wannan zaben na da nasaba da tashin hankali, rashin zuwan kayan zabe, rashin aiki na BIVAS da kuma jawo hankalin jama’a ta fuskoki daban-daban.
Da yake mayar da martani, Kwamishinan Zabe na Jihar, Alhaji Ahmed Bello-Mahmud, ya bayyana jin dadinsa da cewa an gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali, adalci, gaskiya da kuma kammalawa ba tare da wata tangarda ba.
Ya kuma yi kira ga masu zabe da su ci gaba da gudanar da zabuka masu zuwa domin amfanin kowa.