Gwamnatin Tarayya ta ja kunnen tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a kan kalamansa da ya yi kan zaben shugaban kasa na 2023 na kokarin tunzura mutane.
Gargadin na a cikin sanarwar da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ya fitar a ranar Talata.
- INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Sanatan Zamfara Ta Tsakiya Bai Kammala Ba
- NNPP Ta Musanta Yarjejeniyar Yi Wa Abduljabbar Yafiya Idan Ta Ci Zaben Gwamna A Kano
Sanarwar, ta ce kalaman na Obasanjo na kiran da ya yi a zauna lafiya manufa ce kawai ta tunzura ‘yan Nijeriya don su yi bore.
Sanarwar wacce ministan ya fitar a Abuja, gwamnatin ta nuna takaicinta kan zarge-zargen da Obasanjo ya yi a kan zaben.
A cewar sanarwar, a lokacin mulkin Obasanjo ne ya gudanar da gurbataccen zabukan da ba a taba yin irin su ba, tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999.
Sanarwar ta ce a yayin da ake kan tsimayin sakamakon zabukan da aka gurfanar duk da cewa, wasu marasa kishi na kokarin kawo rudani kan zabukan ta hanyar kalamansu, kamata ya yi bisa ikirarin na Obasanjo na cewa shi dattijo ne, da sai ya yi amfani da danjitakarsa wajen kwantar wuta amma ba rura wutar ba.
Sanarwar ta ce, hada zabukan a Nijeriya ba karamin aiki bane idan aka yi la’akari da yawan adadin alumma 93,469,008 a kasar ya fi yawan adadi 16,742,916 na wandanda aka yiwa rijista da suka kai yawan 76,726,092 Afirka ta yamma.
A cewar sanarwar, yadda aka tura jami’an zabe sama da 1,265,227 da yin amfani da kayan zabe na zamani don a gudanar da sahihin zabe, wannan ya nuna irin kokarin da hukumar zabe INEC ta yi don gudanar amintaccen zabe, wanda rahoton hukumar ECOWAS da ta sa ido kan yadda aka yi zaben ya tabbatar da hakan.