Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta tsare wani zababben dan majalisa a zaben 2023 da aka kammala a karkashin jam’iyyar NNPP Aliyu Madakin Gini, bisa laifin mallakar makami ba bisa ka’ida ba.
An zabi Madaki ne a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Dala ta jihar Kano a majalisar wakilai ta 10.
‘Yansanda Sun Hana Jam’iyyu Siyasa Zagayen Murnar Nasarar Cin Zabe A Jihar Kebbi
LEADERSHIP ta samu labarin cewa, Madaki ya mutunta gayyatar ‘yansanda wacce suka yi masa a ranar Laraba bayan ganin yadda hotunansa suka yadu a shafukan sada zumunta dauke da bindiga a lokacin wani gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Engr. Rabiu Kwankwaso, a makon da ya gabata.
Idan ba a manta ba a ranar 23 ga watan Fabrairu ne wasu ‘yan bangar siyasa dauke da makamai suka kai hari kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a kan titin zuwa Zaria a Kano, a lokacin babban taron yakin neman zabensa na shugaban kasa, kuma an ce Madaki ne ya jagoranci tawagar da suka fatattaki ‘yan bangar siyasar.
Lamarin wanda ya kai ga jami’an tsaro sun cafke shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomin Ungogo da Rimingado na jihar, Abdullahi Ramat da Munir Dahiru suma dauke da bindigu.
An kuma rahoto, ‘yansanda sun kama wasu ‘yan daba 85 a lokacin gangamin yakin neman zaben.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp