Yau Litinin 20 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron bayar da Rahoton Cigaban Duniya ta kafar bidiyo tare da gabatar da jawabi.
A jawabin nasa Wang Yi ya jaddada cewa, bisa hangen nesa da Shugaba Xi Jinping ya yi kan amfana wa dukkanin bil Adama, ya gabatar da shawarar bunkasa duniya a wajen taron majalisar dinkin duniya, da gaggauta aiwatar da ajandar majalisar ta neman samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, a kokarin sa kaimi ga ci gaban duniya yadda ya kamata.
Ban da wannan kuma, Wang Yi ya bayyana cewa, cikin rahoton cigaban duniyar, kasar Sin ta baiwa ajandar MDD shawarwari daga fannoni 8, bisa kyawawan sakamako da fasahohin da Sin da kasashen duniya suka samu.
Wannan shi ne wani muhimmin mataki da kasar Sin ta dauka wajen aiwatar da shawarar bunkasa duniya, wanda zai taimakawa kasa da kasa wajen kara samun bunkasuwa, da ma samar da dabaru ga sha’anin ci gaban duniya.
Kasar Sin na son yin kokari tare da bangarori daban daban wajen aiwatar da shawarar bunkasa duniya, da gaggauta ajandar MDD, a kokarin raya kyakkyawar makomar ci gaban duniya ta bai daya. (Kande Gao)