A jiya Alhamis, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da wani taron manema labaru, dangane da aikin raya kasuwanci ta ingantacciyar hanya. Inda wasu manyan jami’an ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin suka yi tsokaci kan yadda ake janyo hankalin masu zuba jari daga ketare, da habaka ciniki cikin ’yanci, da gudanar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” (B&R) a kasar Sin.
Bayanai na nuna cewa a wannan shekara, za a yi kokarin samun takamaiman sakamako, a yunkurin neman ganin kasar Sin ta sa hannu kan yarjejeniyar huldar abota da ta shafi tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani.
Wasu alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, kasar Sin ta samu damar yin amfani da jari na ketare da yawansa ya kai Yuan triliyan 1.2 (kwatankwacin dalar Amurka biliyan 174) a shekarar 2022, adadin da ya karu da kashi 6.3% idan an kwatanta da na bara.
Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta ce za ta yi la’akari da matakan takaita kayyade shigo da jarin ketare cikin kasuwannin kasar Sin, don aiwatar da manufar kasar Sin ta bude kofarta ga kasashen waje yadda ake bukata.
Bana shekaru goma ke nan, tun bayan da aka gabatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”. A cewar ma’aikatar kasuwancin Sin, za ta sa kaimi ga kulla yarjejeniyar ciniki cikin ’yanci da karin kasashen da suka shiga shirin “Ziri Daya da Hanya Daya”. (Bello Wang)