Da safiyar yau Asabar ne, agogon Beijing, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC), dake zama babbar majalisar tsara dokokin kasar, ta gudanar da taron manema labarai, gabanin bude taronta na shekara-shekara, inda mai magana da yawun taron, Mr. Wang Chao ya bayyana cewa, kasar Sin ba ita ce kasar da ta fi kowacce kasa bayar da bashi ga kasashen Afirka ba.
Wang Chao ya ce, kamar yadda alkaluma daga bankin duniya suka nuna cewa, kusan kashi uku bisa hudu na bashin da ake bin kasashen Afirka, sun fito ne daga cibiyoyin hada-hadar kudi mallakar bangarori daban daban da masu lamuni na kasuwanci. Har kullum kasar Sin ta himmatu wajen taimakawa kasashen Afirka rage bashin da ake bin su. Mr. Wang Chao yana mai karyata ikirarin cewa, wai kasar Sin na haifar da abin da ake kira “tarkon bashi” a Afirka.
- Kenya Za Ta Fara Hada Motocin Bas-bas Masu Amfani Da Wutar Lantarki 130 Na Kasar Sin A Shekarar 2023
Sannan Mr. Wang Chao ya sanar da cewa, da misalin karfe 9 na safiyar gobe Lahadi ne, aka tsara za a bude taron farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, kana za a kammala shi a ranar 13 ga wata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
A cewar Wang, a yayin taron farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, baya ga nazarin jerin rahotanni da suka hada da rahoton aikin gwamnati, ana sa ran wakilan NPC za su tattauna kan daftarin shirin gyaran dokar kafa dokoki da kuma shirin yin garambawul ga hukumomin majalisar gudanarwar kasar.
Bugu da kari, Wang Chao ya ce, kasar Sin tana mai da hankali matuka, kan inganta tsarin doka game da kara bude kofa ga kasashen ketare, bugu da kari, kasar Sin ta kudiri aniyar ciyar da sha’anin doka gaba a fannin kiyaye muradun ikon mulkin kasa da tsaro, da samun bunkasuwa. (Ibrahim Yaya)