Kakakin tawagar sojojin ‘yantar da jama’a da ‘yan sanda dake halartar taron farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 Tan Kefei, ya amsa tambayoyi daga ‘yan jarida game da kasafin kudin Sin kan tsaron kasa.
Tan Kefei ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar tabbatar da tsaron kasa tare da bunkasuwar tattalin arziki, kuma an tabbatar da yawan kudin da za a kashe kan tsaron kasa ne bisa bukatun tsaron kasa da yanayin bunkasuwar tattalin arziki. Ya ce kasafin kudin Sin kan tsaron kasa a shekarar 2023 ya kai kudin Sin RMB Yuan triliyan 1.58, wanda ya karu da kashi 7.2 cikin dari bisa na shekarar bara.
A cewarsa, Sin ta dukufa wajen bin hanyar samun ci gaba cikin lumana, da aiwatar da manufofin tabbatar da tsaron kasa, amma ba ta hanyar kai hari da farko ba.
Idan aka kwatanta da kasar Amurka a wannan fanni, kudin da Sin ta kashe kan tsaron kasa, ba shi da yawa cikin yawan GDPnta da dukkan kudin kashewarta, kana kudin tsaron kasa da aka kashe kan kowanne mutum ko kowane jami’in tsaro, ba shi da yawa.
Ya kara da cewa, Sin ta kashe kudi kan tsaron kasa don tabbatar da ikon mallakar yankunanta da tsaro da moriyar bunkasuwar kasar. (Zainab)